Jump to content

Abubakar Momoh

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar Momoh
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 - Johnson Oghuma (en) Fassara
District: Etsako East/Etsako West/Etsako Central
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yaren afenmai
Karatu
Harsuna Turanci
pidgin
Yaren afenmai
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Abubakar Momoh ɗan siyasan Najeriya ne kuma injiniya. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa shi minista a hukumar raya Neja Delta. Ya kasance tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Edo kuma tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Etsako, a jihar Edo. [1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Abubakar daga. Imiegba, North Ibie, Etsako East LGA of Edo State yake. Ya kammala karatunsa a jami'ar Benin inda ya karanci ilimin kimiyyar sinadarai. Ya kuma sami digiri na biyu a fannin injiniyan sinadarai daga Jami'ar Legas da kuma digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati daga Jami'ar Ambrose Ali da ke Ekpoma.

Shi ma'aikaci ne a Cibiyar Gudanar da Harkokin Jama'a (FPA) kuma memba ne mai rijista a kungiyar Injiniya ta Najeriya da kuma Majalisar Dokokin Injiniya a Najeriya (COREN).

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Abubakar Momoh ya fara siyasa ne a matsayin kansila zuwa shugaban ƙaramar hukuma. A shekarar 1999-2003 ya zama ɗan majalisa a majalisar dokokin jihar Edo kafin ya je tarayya ya yi aiki a mazaɓar tarayya ta Etsako tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007. An kuma zaɓe shi a karo na biyu a matsayin ɗan majalisar wakilai tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015. Ya sauya sheka a shekarar 2019 ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) don neman kujerar Sanatan Edo ta Arewa amma ya faɗi zaɓe. Daga baya ya koma jam’iyyarsa ta APC. A shekarar 2023, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Abubakar Momoh a matsayin ministan raya yankin Neja Delta. [2] [3] [4]

  1. Akintayo, Kabir (2023-08-17). "Tinubu Appoints 62-year-old Abubakar Momoh as Youth Minister". Politics Digest (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.
  2. Effiong, Sarah (2023-08-30). "Abubakkar Momoh; biography, education, career and politics". platinumtimes.ng (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.
  3. Akintayo, Kabir (2023-08-17). "Tinubu Appoints 62-year-old Abubakar Momoh as Youth Minister". Politics Digest (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.
  4. "Tinubu Brings Back Niger Delta Development Ministry, Names Momoh Minister-designate – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2023-10-27.