Jump to content

Adebowale Adefuye

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adebowale Adefuye, Ambassador of Nigeria to the United States
Adefuye yayin ziyarar da ya kai fadar White House ranar 29 ga Maris, 2010

Adebowale Ibidapo Adefuye (an haife shi a ranar 27 ga watan Janairu shekarata alif 1947 zuwa watan Agusta a ranar 27 shekarar 2015) masanin tarihin Najeriya ne kuma jami'in diflomasiyya.

Aikin ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Ijebu-Igbo, Adefuye ya halarci Jami'ar Ibadan, ya kamala karatunsa a shekarar 1969. Ya samu digirin digirgir (Ph.D) a tarihi daga wannan cibiyar a shekarar 1973. A lokacin aikinsa na ilimi, Adefuye an ba shi suna Fulbright Scholar kuma ya yi amfani da kudaden don yin bincike a Jami'ar Columbia, Jami'ar North Florida, da Jami'ar Florida . Adefuye ya koyar a Jami’ar Legas, inda ya jagoranci sashen tarihin makarantar daga shaekarar 1985 zuwa shekara ta 1987. [1]

Aikin diflomasiyya

[gyara sashe | gyara masomin]

An nada shi Ambasada a Jamaica a shekara ta 1987, yana aiki har zuwa shekarar 1991. A wannan lokacin, Adefuye kuma ya kasance jakada a Belize da Haiti a lokaci guda. Sannan ya kasance mataimakin babban kwamishina a kasar Ingila. Adefuye ya bar wannan mukamin ya zama mataimakin daraktan kungiyar Commonwealth na tsawon shekaru goma sha hudu. Bayan ya bar Commonwealth, ya zama mai ba da shawara ga Ƙungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka a shekara ta 2008. Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Adefuye jakada a Amurka a shekarar 2010. A lokacin mulkinsa, Adefuye ya ci gaba da ba da shawarar cewa Amurka ta ba da karin taimakon soja ga Najeriya don murkushe mayakan Boko Haram yadda ya kamata. A shekarar 2015 ne aka sake kiransa bayan an rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya .

Ya mutu a Washington, DC a ranar 27 ga watan Agusta, shekarar 2015, sakamakon bugun zuciya.

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named SahRep