Adesimbo Victor Kiladejo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adesimbo Victor Kiladejo
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta University of Liverpool (en) Fassara
Jami'ar Obafemi Awolowo
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a likita

Oba Adesimbo Victor Kiladejo Adenrele Ademefun Kiladejo, ko Jilo III, an naɗa shi Osemawe na 44, ko kuma sarkin gargajiya na Masarautar Ondo a Najeriya a ranar 1 ga Disamba 2006. An naɗa shi sarautar ne a ranar 29 ga Disamba 2008 a wani biki da ya samu halartar manyan baki da suka haɗa da gwamnan jihar Ondo, Olusegun Agagu, Ooni na Ife, Oba Okunade Sijuade, da shugaban ƙungiyar Afenifere, Cif Reuben Fasoranti.[1]

Rayuwar farko da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Kiladejo a garin Ondo, shi ne babba a cikin ‘ya’ya ashirin da biyu na Yarima Gbadebo Adedoyin Kiladejo, Edilokun na gidan sarautar Okuta. Ya halarci Jami'ar Ife, yanzu Jami'ar Obafemi Awolowo, inda ya sami digiri na farko (B.Sc.) a fannin kiwon lafiya, (Bachelor of Medicine da Bachelor of Surgery). Ya tafi Jami'ar Liverpool don karatun digiri na biyu akan lafiyar haihuwa. Bayan aikin sa na matasa, ya fara aiki a hukumar kula da lafiya ta jihar Ondo, inda ya kai mmatsayin daraktan kiwon lafiya. Ya bar aikin sa na sirri, Kiladejo Hospitals Group a Ikere Ekiti, kuma daga baya ya shiga harkar kasuwanci.[2]

Mulki[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa Kiladejo a ranar 29 ga Disamba 2008 a mmatsayin Osemawe na Ondo na uku da ya fito daga layin Jilo na Okuta Ruling House, na biyu shine Arojojoye Oba Pupa, wanda ya yi mulki daga 1926 zuwa 1935. Gidan Okuta ya fito ne daga Oba Luju, wanda ya yi sarauta tsakanin 1561 zuwa 1590 kuma ɗan sarkin Ondo na farko, Oba Pupupu.[3] Bayan hawan sa, Kiladejo ya ɓullo da tsarin sarrafa na’ura mai kwakwalwa a cikin mulkin masarautan, ya inganta lafiya a tsakanin talakawansa, ya kafa kwamitoci don warware matsalolin tsaro da rigingimun filaye.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. HOPE AFOKE ORIVRI (30 December 2008). "Ondo stands still for 44th Osemawe". Nigerian Compass. Retrieved 2010-09-14.
  2. "Biography of His Royal Majesty". The Osemawe and Paramount Ruler of Ondo Kingdom. Retrieved 2010-09-14.
  3. "500 years of the Osemawe Dynasty". The Punch. 2010-07-02. Archived from the original on 2011-07-28. Retrieved 2010-09-14.
  4. SUNDAY ABORISADE (6 Dec 2009). "I miss my freedom – Osemawe". The Punch. Archived from the original on 2009-12-07. Retrieved 2010-09-14.