Jump to content

Adeyemi Ikuforiji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adeyemi Ikuforiji
Rayuwa
Haihuwa jahar Legas, 24 ga Augusta, 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Babeș-Bolyai University (en) Fassara
Jami'ar jahar Lagos
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
adeyemiikuforiji.org

Sabit Adeyemi Ikuforiji ( ⓘ ) ; an haife shi ranar 24 ga Agusta 1958) masanin tattalin arzikin Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda ya zama kakakin majalisar dokokin jihar Legas daga shekarar 2005 zuwa 2015.[1][2] An gurfanar da shi ne tare da tsohon mataimakinsa Oyebode Atoyebi a kan tuhume-tuhume 54 na karkatar da kuɗaɗen da suka kai Naira miliyan 333.8, daga bisani an wanke shi daga zargin.[3][4]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sabit Adeyemi Ikuforiji a ranar 24 ga watan Agustan 1958 a Epe, ƙaramar hukumar jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya. Ya halarci Makarantar Local Authority Central a Epe kafin ya wuce makarantar Epe Grammar inda ya sami takardar shedar Makarantar Yammacin Afirka a watan Yuli 1975.[5] Ya sami digiri na farko da na biyu a fannin tattalin arziki daga Jami'ar Babeș-Bolyai da Bucharest Academy of Economic Studies.[6] Daga baya ya samu digirin digirgir a fannin kasuwanci a jami’ar Legas a shekarar 1980.[7]

Ya fara harkar siyasa a matsayin babban sakataren jam'iyyar Unity Party of Nigeria. A shekarar 2003, ya tsaya takarar kujerar mazaɓarsa, Epe Constituency I, aka zaɓe shi, dan majalisar dokokin jihar Legas.[8] A cikin watan Disamba 2005, an zaɓe shi a matsayin kakakin majalisa a ƙarƙashin jam'iyar Alliance for Democracy.[9] A ranar 4 ga watan Yunin 2007 aka sake zaɓen shi a karo na biyu a matsayin kakakin majalisa ta 6 bayan ya fito a matsayin wanda ya lashe zaɓen daga mazaɓarsa.[10]

Har wayau a ranar 4 ga watan Yunin 2011 an sake zaɓen shi a karo na uku a matsayin kakakin majalissar ta 7, wanda ya yi mulki har zuwa 3 ga watan Yuni 2015.[11]

  1. "Ikuforiji Re-elected Lagos Speaker, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
  2. "I don't need any petition to impeach Fashola -Ikuforiji". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
  3. "2015 Gov Race: I Want To Succeed Fashola, Says Ikuforiji - P.M. NEWS Nigeria". pmnewsnigeria.com. Retrieved 18 April 2015.
  4. "Alleged money laundering: EFCC closes case against former Lagos Speaker, Ikuforiji" (in Turanci). 2021-03-17. Retrieved 2022-02-07.
  5. Leadership Newspaper (15 November 2014). "Lagos 2015: Ikufuriji, Hamzat, Ambode Battle To Clinch APC Ticket". Nigerian News from Leadership News. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
  6. "THE DAY I GOT A SCHOLARSHIP, MY POOR DAD DANCED NAKED –HON. ADEYEMI IKUFORIJI". nigerianbestforum.com. Retrieved 18 April 2015.
  7. "At 54, Lagos Speaker Ikuforiji Trudges On, Articles - THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
  8. "Ikuforiji Willing To Succeed Babtunde Fashola In 2015". naij.com. Retrieved 18 April 2015.
  9. Bright Owusu. "Ikuforiji re-elected speaker as Lagos inaugurates 7th Assembly". Ghanamma.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
  10. "Lagos 2015-why the next gov should be Ikuforiji". Tribune.com. Archived from the original on 18 April 2015. Retrieved 18 April 2015.
  11. "Lagos state house of Assembly: Ikuforiji re-elected speaker". theinfostride.com. Retrieved 18 April 2015.