Ado Gwanja
Ado Gwanja | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Kano, 1990 (33/34 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo, jarumi, mai tsara fim da mawaƙi |
Kayan kida | murya |
Imani | |
Addini | Musulmi |
Ado Isah Gwanja (an haife shi a ranar 22 ga watan Janairun shekarar alif 1990) a unguwar Briget da ke Kano. Gwanja mawaki ne kuma jarumi a masana’antar fina-finan Arewacin Najeriya da aka fi sani da Kannywood . Gwanja fitaccen mawaki ne da wakokinsa suka shahara musamman a tsakanin mata da matasa a Arewacin Najeriya.
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Gwanja dai ya fara fitowa a fina-finai ne a shekarar 2017, amma ya ɗauki tsawon lokaci a harkar waka kafin ya fara wasan kwaikwayo. Gwanja sau da yawa an fi saninsa a waka fiye da a fim. Gwanja ya ƙware a wakokinsa na mata, ana gayyatarsa zuwa bukukuwa inda yake rera waƙoƙinsa. Gwanja ya nada tsohon mawakin Hausa Aminu Mai Dawayya a matsayin jagoransa.
Wasu daga cikin wakokin Gwanja da suka yi fice sun hada da Kujerar Tsakar Gida, Mamar-Mamar, Dakin Bakuwa, Asha Rwa-rawa, Kilu ta Ja Bau, Kidan Mata da sauran su.
Kundin Waka
[gyara sashe | gyara masomin]Kundi wakokin Gwanja kenan;
Fim | Shekara |
---|---|
Kujerar Tsakar Gida | 2014 |
Indosa | 2017 |
Matan Arewa | 2016 |
Juya | 2018 |
Ga Gwanja | 2017 |
Tangaran | 2021 |
Adama | 2021 |
Dakatarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Hukumar kula da kafafen sadarwa ta BBC a Nijeriya ta haramta waƙar 'Warr' ta Ado Gwanja a Najeriya dama sanya waƙar a gidajen rediyo ta telebijin.
A sanarwar da NBC ta fitar ta ce waƙar 'Warr' ta bayyana rashin tarbiyya da kalaman da ba su dace ba.
Hukumar tayi zargin cewar a cikin waƙar akwai zagi kai tsaye da kuma nuna yadda wasu ke tangadi bayan sun bugu da barasa ko kuma giya.[1]
Ko a baya-bayan nan da shahararren mawakin ya fitar da wata waƙa mai taken Chass wadda ita ma ta tada ƙura. Har takai ga hakumar tace finafinai ta nemi shi [2]
Fina-finnai
[gyara sashe | gyara masomin]Ado baya ga kasancewar sa mawakin kuma yana fitowa acikin finafinai na masana'antar kannywood. Ka kaɗan daga cikin wasu;
- Gidan badamasi
- Ukku sau ukku
- Dan kuka
- Dankuka a birni
- Dan yau
- Daga murna. da sauransu
Kyaututtuka
[gyara sashe | gyara masomin]Gwanja ya samu kyaututtuka da dama daga daidaikun mutane da kungiyoyi. Daga cikin manyan lambobin yabo da Gwanja ya samu akwai lambar yabo da uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bayar. Sauran kyaututtukan da suka hada da;
Shekara | Kyauta | Rukuni | Sakamako |
---|---|---|---|
2019 | Samun lambar yabo ta Kano | Nasara | |
2018 | Sani Abacha Youth Center Award | Nasara | |
2018 | Ƙungiyar Dalibai ta ƙasa (NANS) | Nasara | |
2019 | RS Fans Entertainment | Nasara | |
2018 | Fitattun Mawakan Hausa | Nasara |
Rayuwa ta kashi kai
[gyara sashe | gyara masomin]Mahaifin Ado Gwanja Bahaushe ne dan Jihar Kano kuma mahaifiyarsa ‘yar asali kabilar Shuwa Arabia ce daga jihar Borno. Gwanja musulmi ne, ya auri mace daya.