Ahmed Ibrahim (Dan siyasar Ghana)
Ahmed Ibrahim dan siyasan Ghana ne kuma dan majalisar wakilai ta bakwai a jamhuriyar Ghana ta hudu mai wakiltar mazabar Banda a yankin Bono a kan tikitin National Democratic Congress.[1][2][3] A halin yanzu shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dokokin Ghana.[4][5]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ibrahim a ranar 6 ga watan Mayun shekarar 1974, a Banda Ahenkro a yankin Bono na kasar Ghana. Ibrahim ya yi karatu a jami'ar Ghana inda ya sami digiri na farko a fannin kimiyyar siyasa da falsafa a shekarar 2001.[6]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ya kasance babban jami'in gudanarwa na Flamingo Publications (Ghana) Limited.[7]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ibrahim ya fara harkar siyasa a shekarar 2009. bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kasar Ghana na shekarar 2008.na mazabarsa. Daga nan ne aka zabe shi a majalisar dokoki ta 5 a jamhuriya ta 4 ta Ghana a ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2009. Bayan kammala wa'adin mulkinsa na farko, Ibrahim ya yanke shawarar sake tsayawa takara a shekara ta 2013. inda ya doke Joe Danquah ya ci gaba da rike kujerarsa. A shekarar 2015. ya tsaya takara kuma ya lashe zaben fidda gwani na majalisar dokokin NDC na mazabar Banda a yankin Bono na Ghana. Ya lashe wannan kujera ta majalisar dokoki a lokacin babban zaben Ghana na 2016 inda ya samu kuri'u 6,167 da ke wakiltar kashi 52.03% yayin da abokin hamayyarsa ya samu kuri'u 5,660 wanda ke wakiltar kashi 47.76%.[7][8]
Kwamitoci
[gyara sashe | gyara masomin]Ibrahim mamba ne a kwamitin kasafin kudi na musamman; memba na kwamitin sadarwa; mamba a kwamitin raya karkara da kananan hukumomi; kuma memba na kwamitin kasuwanci.[6]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Ibrahim Kirista ne.[6] Yana da aure da yaro daya.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Minority fumes over bill to put COCOBOD under Agric Ministry; says it is needless". The Chronicle Online (in Turanci). 2020-10-08. Archived from the original on 2021-01-14. Retrieved 2021-01-12.
- ↑ "Banda MP donates 12,000 blocks to four churches". The Chronicle Online (in Turanci). 2020-12-17. Archived from the original on 2021-01-31. Retrieved 2021-01-12.
- ↑ "E-levy not on Parliament's business statement for this week - Ahmed Ibrahim - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). 2022-01-25. Retrieved 2022-11-13.
- ↑ "Ahmed Ibrahim raises concerns over nomination of Justice Gaewu to Supreme Court bench". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2022-08-02. Retrieved 2022-11-13.
- ↑ Tornyi, Emmanuel (2022-09-30). "National Security warned Nana Addo against SIM card blockage – Ahmed Ibrahim". Pulse Ghana (in Turanci). Retrieved 2022-11-13.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2022-11-13.
- ↑ 7.0 7.1 7.2 "Ghana MPs - List of MPs". www.ghanamps.com. Retrieved 2019-03-12.
- ↑ FM, Peace. "Parliament - Banda Constituency Election 2016 Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-12-06.