Oudjani ya kasance memba a ƙungiyar FLN ta Aljeriya kafin ƙasar ta samu 'yancin kai. Shi ne kuma wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin RC Lens, inda ya zura ƙwallaye 94 a wasanni 148 da ya buga wa ƙungiyar, ciki har da ƙwallaye 6 a wasa daya da suka yi da RC Paris a kakar 1963/1964. Ya zura ƙwallaye 99 a raga a gasar Ligue 1, kuma shi ne ya fi zura ƙwallaye a gasar 1963–64 ta Faransa da ƙwallaye 30.[1][2]
Ahmed shi ne mahaifin tsohon ɗan wasan Aljeriya Cherif Oudjani, wanda ya zura ƙwallon da ta yi nasara a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1990 .
Ahmed Oudjani
Iyalin Ahmed 'yan asalin Kabyl ne, kuma sun fito daga ƙauyen Sidi Aïch a Bejaïa .