Jump to content

Alhassan Mohammed Gani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alhassan Mohammed Gani
Rayuwa
Haihuwa 1959
ƙasa Najeriya
Mutuwa 27 ga Yuli, 2025
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jos
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami

Alhassan Mohammed Gani (1959–2025) wani malamin makaranta ne kuma mai gudanarwa a Najeriya. wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban jami'yar tarayya Kashere, a jihar Gombe.[1][2][3]

An haifi Gani a shekarar 1959 a Delgi, karamar hukumar jihar Filato. Ya fara karatun sa na farko a makarantar firamare, Delgi daga 1966 zuwa 1973. A 1978 ya sami B.Sc a Botany tare da babban aji daga Jami'ar Jos a shekarun 1980 zuwa 1984.[3]

Gani ya je jami’ar Landan inda ya samu takardar shaidar M.Sc a fannin kimiyyar tsire-tsire a shekarar 1988. Sannan ya yi digirinsa na uku a fannin ilimin kimiyyar tsire-tsire a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Ya zama farfesa a can a 2006.[3]

  1. "Professor Alhassan Mohammed Gani – Channels Television". Retrieved 2021-02-15.
  2. "Prof. Gani's good leadership story at Fuk". Daily Trust (in Turanci). 14 October 2020. Retrieved 2021-02-15.
  3. 3.0 3.1 3.2 IV, Editorial (2021-02-10). "As a quintessential VC, Gani, bows out of Kashere…". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2021-02-15.