Ali Yusuf Kenadid
Ali Yusuf Kenadid | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Daular Musulunci ta Hobyo | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Yusuf Ali Kenadid | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Ali Yusuf Kenadid ( Somali , Larabci: علي يوسف كينايديض ) ya kasance sarki Somaliya na zamanin baya. Ya kasance sarki na biyu a masarautar Daular Musulunci ta Hobyo.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ali Yusuf a gidan Darod na Majeerteen. Mahaifinsa shine Sultan Yusuf Ali Kenadid, shi ne wanda ya kafa masarautar Daular Musulunci ta Hobyo mai cibiya a arewa maso gabas da tsakiyar Somaliya a yau. An kafa mulkin ne a cikin shekarar 1870s akan yankin da aka zana daga Majeerteen Sultanate (Migiurtinia). [1] Ɗan'uwan Ali Yusuf, Osman Yusuf Kenadid, zai ci gaba da ƙirƙirar rubutun Osmanya don yaren Somaliya[2]
A yunƙurinsa na cigaba da manufofinsa na faɗaɗa daularsa, Kenadid père a ƙarshen shekarar 1888 ya shiga yarjejeniya da Italiya, ya mai da mulkinsa karkashin kariyar Italiya.[3] Sharuɗɗan yarjejeniyar sun bayyana cewa Italiya za ta kawar da duk wanda ya tsoma baki a cikin harkokin mulkin sultan.[4]
Sai dai alaƙar da ke tsakanin Hobyo da Italiya ta yi tsami a lokacin da dattijan Kenadid suka ki amincewa da shawarar turawan Italiya na ba wa tawagar sojojin Birtaniya damar sauka a cikin masarautarsa domin su ci gaba da yaƙin su da dakarun Derwish na Mohammed Abdullah Hassan.[3] Daga nan aka kori Ali Yusuf da mahaifinsa zuwa Eritrea.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Helen Chapin Metz, ed., Somalia: a country study, (The Division: 1993), p.10.
- ↑ Diringer, David (1968). The Alphabet: A Key to the History of Mankind, Volume 1. Funk & Wagnalls. pp. 235–236. ISBN 1452299374. Retrieved 14 December 2014.
- ↑ 3.0 3.1 The Majeerteen Sultanates
- ↑ Issa-Salwe, Abdisalam M. (1996). The Collapse of the Somali State: The Impact of the Colonial Legacy. London: Haan Associates. pp. 34–35. ISBN 187420991X.