Aliero
Appearance
Aliero | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Yawan mutane | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Aliero birni ne, da ke cikin jihar Kebbi a arewacin Najeriya. Dake cikin kudu maso gabashin jihar Kebbi.
Tattalin Arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Yawancin mutanen ƙaramar hukumar Aliero manoma ne, tare da mai da hankali kan kayan lambu, musamman albasa da barkono. Garin yana da kasuwar albasa mafi girma a arewa maso yammacin Najeriya, kuma ita ce kuma babbar kasuwar albasa a Najeriya. Mazauna Aliero an san su da sa himma a Yammaci da Tsakiyar Afirka. Garin Aliero yana kewaye da bishiyoyin mangwaro .