Ambaliyar Accra ta 2022

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ambaliyar Accra ta 2022

A ranar Lahadi 5 ga watan Yuni, shekarar 2022, an mamaye wasu sassa na Accra yayin da ake ruwan sama. [1] Ruwan saman da ya kwashe kusan sa'o'i huɗu ya bar baya da ƙura a yankuna kamar Kaneshie, wanda ya fi ƙamari bayan ruwan sama.

Wasu daga cikin yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Kwame Nkrumah Circle, Spintex Road, Tetteh Quarshe, Fiesta Royal da Nsawam Road.[2]

Sakamakon ambaliyar ruwa a birnin Accra, shugaba Akufo-Addo ya umurci hukumomin birnin da majalisun gundumomi (MMDAs) na yankin Greater Accra da su rusa dukkan gine-ginen da ke kan hanyar kogin da ke haddasa ambaliya a cikin birnin.[3]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • 2015 Ambaliyar Accra
  • 2016 Ambaliyar Accra

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Parts of Accra flooded again after downpour". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2022-06-05. Retrieved 2022-07-25.
  2. "Parts of Accra flooded again, social media users react". GhanaWeb (in Turanci). 2022-07-05. Archived from the original on 2022-07-25. Retrieved 2022-07-25.
  3. "Parts of Accra flooded again after downpour". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2022-06-05. Retrieved 2022-07-25.