Angelina Jolie
![]() | |||
---|---|---|---|
![]() | |||
27 ga Augusta, 2001 - | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Angelina Jolie Voight | ||
Haihuwa | Los Angeles, 4 ga Yuni, 1975 (48 shekaru) | ||
ƙasa |
Tarayyar Amurka Kambodiya | ||
Mazauni |
Los Angeles Palisades (en) ![]() | ||
Harshen uwa |
Turancin Amurka Turanci | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Jon Voight | ||
Mahaifiya | Marcheline Bertrand | ||
Abokiyar zama |
Jonny Lee Miller (en) ![]() Billy Bob Thornton (en) ![]() Brad Pitt (en) ![]() | ||
Ma'aurata |
Jenny Shimizu (en) ![]() Brad Pitt (en) ![]() | ||
Yara |
view
| ||
Ahali |
James Haven (en) ![]() | ||
Ƴan uwa |
view
| ||
Karatu | |||
Makaranta |
Beverly Hills High School (en) ![]() Lee Strasberg Theatre and Film Institute (en) ![]() New York University (en) ![]() Tappan Zee High School (en) ![]() | ||
Harsuna |
Turanci Turancin Amurka Khmer (en) ![]() | ||
Sana'a | |||
Sana'a |
ɗan wasan kwaikwayo, darakta, mai tsara fim, model (en) ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() | ||
Tsayi | 169 cm | ||
Employers | UNICEF | ||
Muhimman ayyuka |
Angelina Jolie filmography (en) ![]() Gia (en) ![]() Girl, Interrupted (en) ![]() Changeling (en) ![]() | ||
Kyaututtuka |
gani
| ||
Ayyanawa daga |
gani
| ||
Mamba |
Clinton Foundation (en) ![]() U.S. Committee for Refugees and Immigrants (en) ![]() Council on Foreign Relations (en) ![]() | ||
Imani | |||
Addini |
lapsed Catholic (en) ![]() | ||
IMDb | nm0001401 |
Angelina Jolie (Lafazi-en|dʒoʊˈliː; née Voight, ada Pitt, an haife ta a watan Yuni 4, 1975)[1] Yar'kasar Tarayyar Amurka ce, yar shiri da hadin fim ce, jaruma, kuma mai taimakon alumma. Ta karba kyautar Academy Award, da Screen Actors Guild Awards guda biyu, da Golden Globe Awards guda uku, kuma ana fadin itace mafi yawan albashi acikin yan'wasan jarumai na Hollywood. Jolie ta fara shirin fim ne tun tana yarinya tareda mahaifinta, Jon Voight, acikin shirin Lookin' to Get Out (1982). Shigarta harkar fim tafara a shekaru goma bayan shirin ta na farko da kamfanin low-budget production Cyborg 2 (1993), sannan yabiyo da babban shirinta data fito na farko, Hackers (1995). Ta fito a fina-finan tarihi na cable George Wallace (1997) da Gia (1998), kuma ta lashe kyautar Academy Award for Best Supporting Actress saboda gudun mawarta acikin dramar Girl, Interrupted (1999).
Jolie ta fito acikin wasannin vidiyo Lara Croft a Lara Croft: Tomb Raider (2001) hakan yazamar da ita amatsayin jagororin jarumai na Hollywood. Ta cigaba da samun nasararta ta jaruma a acikin fina-finan ta da fim din Mr. & Mrs. Smith (2005), Wanted (2008), da Salt (2010), kuma tasamu muhimman shaida saboda gudunmawarta acikin dramomin A Mighty Heart (2007) da Changeling (2008), wadanda suka samar mata da zaben Academy Award for Best Actress. Babban nasarar ta a kasuwanci yazo ne tareda the fantasy picture Maleficent (2014). A shekarun 2010, Jolie ta fadada aikinta da zama darekta, screenwriting, da kuma producing, tareda In the Land of Blood and Honey (2011), Unbroken (2014), By the Sea (2015), da First They Killed My Father (2017). Akan Aikinta na shiryawa da fitowa a fina-finai, Jolie kuma ansan ta da kokarin wurin taimako ga alumma, hakan yasa ta samu karramawan Jean Hersholt Humanitarian Award da kuma honorary damehood of the Order of St Michael and St George (DCMG), tareda da wash karramawa. Ta taimaka yin abubuwan taimako da dama, wanda suka hada da conservation, ilimi, da yancin mata, da kuma ficenta akan rajin hakkin yan'gudun hijira amatsayin Special Envoy na United Nations High Commissioner for Refugees (UNHCR). Amatsayin ta macen alumma, Jolie ana cewar na daga cikin wadanda suka fi karfi da shahara acikin yan'masana'antar nishadantarwa dake Amurka. A tsawon shekaru, an fadi cewar itace macen datafi kowace mace kyau a duniya daga kamfanonin yasa labarai da dama, kuma ke bantattar rayuwarta yazamanto abunda kowa ke sani. Rabuwar aurenta da jarumai Jonny Lee Miller da Billy Bob Thornton, kuma sun rabu da mijinta na uku, jarumi Brad Pitt, a watan September 2016. Suna da yara shida tare, wadanda uku daga cikin yaran rainonsu sukayi daga kasashe daban-daban na duniya.
Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]
Anazarci[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ cite web| url = http://www.biography.com/people/angelina-jolie-9356782 | title=Angelina Jolie Biography: Director, Film Actress (1975–) | publisher=Biography.com (FYI / A&E Networks)| accessdate= November 11, 2015| archivedate = August 25, 2015 | archiveurl = https://web.archive.org/web/20150825185439/http://www.biography.com/people/angelina-jolie-9356782 | deadurl=no