Jump to content

Anna Neethling-Pohl

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anna Neethling-Pohl
Rayuwa
Haihuwa Graaff-Reinet (en) Fassara, 24 Disamba 1906
ƙasa Afirka ta kudu
Mutuwa Bloemfontein, 14 ga Augusta, 1992
Ƴan uwa
Ahali Truida Louw (en) Fassara
Karatu
Harsuna Turanci
Afrikaans
Sana'a
Sana'a jarumi, marubuci da darakta
IMDb nm1293967
Anna Neethling-Pohl

Anna Neethling-Pohl (an haife ta 24 Disamba 1906, Graaff-Reinet - ta mutu 14 ga Agusta 1992, Bloemfontein ) ƴar wasan kwaikwayo ce kuma mai shirya fina-finai ta Afirka ta Kudu. Ita ma marubuciya ce wacce ta rubuta a ƙarƙashin sunan alƙalami Niehausvor da kuma wani lokacin Wynand du Preez. Ita ce mace ta farko mai watsa labarai a gidan rediyon Afirka ta Kudu.[1]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Anna Servasina Pohl a Graaff-Reinet ranar 24 ga watan Disamba, 1906, ita ce babba a cikin yara huɗu. Ta fara gabatar da wasa a gidan wasan kwaikwayo tun tana ƴar shekara biyar kuma ta shiga wasan kwaikwayo na makarantar sakandare a Langenhoven . Ta halarci wasan kwaikwayo fiye da 50 a tsawon rayuwarta, yawancinsu a cikin Afrikaans ne. Daga cikin ayyukanta akwai fassarar wasan kwaikwayo na Shakespeare 7 zuwa Afirkaans.

Mahaifiyarta ta mutu a lokacin babbar annoba ta mura ta Oktoba 1918 kuma jaririn da take dauke da shi bai zo da ra ba. Shekaru biyu bayan mutuwarta, mahaifinta ya auri Johanna le Roux kuma ya haifi ƴaƴa biyu (Pieter le Roux da Friedrich Wilhelm) daga wannan aure. Mahaifinta ya rasu a shekara ta 1964 bayan cika shekaru casa’in da haihuwarsa a duniya.[2]

  1. Women Marching Into the 21st Century: Wathint' Abafazi, Wathint' Imbokodo (in Turanci). HSRC Press. 2000. ISBN 9780796919663.
  2. "Anna Servisina Neethling Pohl". www.geni.com (in Turanci). Retrieved 2017-11-28.

Hanyoyin Hadi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]

Media related to Anna Neethling-Pohl at Wikimedia Commons