Anthea McIntyre

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anthea McIntyre
member of the European Parliament (en) Fassara

2 ga Yuli, 2019 - 31 ga Janairu, 2020
District: West Midlands (en) Fassara
Election: 2019 European Parliament election (en) Fassara
member of the European Parliament (en) Fassara

1 ga Yuli, 2014 - 1 ga Yuli, 2019
District: West Midlands (en) Fassara
Election: 2014 European Parliament election (en) Fassara
member of the European Parliament (en) Fassara

1 Disamba 2011 - 30 ga Yuni, 2014
Philip Bushill-Matthews (en) Fassara
District: West Midlands (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Landan, 29 ga Yuni, 1954 (69 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Harshen uwa Turanci
Karatu
Makaranta Claremont Fan Court School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da ɗan kasuwa
Wurin aiki Strasbourg da City of Brussels (en) Fassara
Kyaututtuka
Imani
Jam'iyar siyasa Conservative Party (en) Fassara
Anthea Elizabeth Joy McIntyre
UK Conservative MEPs with EU Commissioner-Designate Lord Hill

Anthea Elizabeth Joy McIntyre, CBE (an haife ta a ranar 29 Yunin shekara ta alif ɗari tara da hamsin da hudu 1954A.c) yar siyasar Jam'iyyar Conservative ce a Biritaniya wacce ta yi aiki a matsayin 'yar Majalisar Tarayyar Turai a mazabar West Midlands tsakanin 2011 zuwa 2020.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta a Landan, 'ya ce ga David Scott McIntyre da Joy Irma Stratford McIntyre, ta yi karatu a Makarantar Claremont na kudi, Esher, sannan kuma Queen's College, London. A matsayinta na 'yar kasuwa a Ross-on-Wye, ta kasance aminiyar kasuwanci a gidajen haya na Wythall Estate tun 1976; a 1985 ta zama mai ba da shawara tare da masu ba da shawara na MCP Management, sannan ta kasance abokiyar hulda a kamfanin daga 1991 zuwa 2011. [1]

McIntyre ta tsaya takarar majalisa a karkashin jam'iyyar Conservative a mazabar Redditch a babban zabe na alif 1997 da Shrewsbury da Atcham a babban zaben 2001. Har ila yau, ba ta yi nasara ba a matsayinta na 'yar takarar Conservative a zaben Turai na 2009 na mazabar West Midlands, amma acikin watan Disamban 2011 an nada ta matsayin mamba na wannan yanki a majalisar Turai ba tare da sake zabe ba. Wannan ya faru ne saboda yerjejeniyar Lisbon cewa ta kara girman majalisar Tarayyar Turai zuwa goma sha takwas, kuma daya daga cikin sabbin kujerun ya zo Burtaniya. Biritaniya ta yanke shawarar ware wannan ga mazabar yankin West Midlands, bisa kididdigar yawan jama'a. Daga nan ne aka yi la'akari da sakamakon zabukan Turai na 2009 don yanke shawarar wanda zai maye kujerar idan an kara. Hakan yasa aka mika wa McIntyre.[ana buƙatar hujja]

Ta yi aiki a kwamitin Majalisar Turai akan ayyukan yi da zamantakewa wato "European Parliament Committee on Employment and Social Affairs" kuma a matsayin memba na majalisar Delegation for Relations with South Africa.

An ba McIntyre lamban girma na "Commander of the Order of the British Empire" (CBE) a lambar yabo na Shekarar 2022 New Year Honours don hidimar siyasa da jama'a. [2]

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1999 McIntyre tayi aurie da Frank Myers, MBE. Tana zaune a Walford, Ross-on-Wye . [1]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 ‘McINTYRE, Anthea Elizabeth Joy', in Who's Who 2013 (London: A. & C. Black, 2013)
  2. "No. 63571". The London Gazette (Supplement). 1 January 2022. p. N9.