Jump to content

Anthony Ani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anthony Ani
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Anthony
Shekarun haihuwa 1936
Harsuna Turanci da Pidgin na Najeriya
Sana'a ɗan siyasa da accountant (en) Fassara
Muƙamin da ya riƙe Ministan Albarkatun kasa

Etubom Anthony Ani ya kasance ƙaramin ministan harkokin waje kuma ministan kuɗi na Najeriya daga shekarar 1994, zuwa 1998, a lokacin mulkin Sani Abacha. [1] Ya fito ne daga ƙaramar hukumar Odukpani da ke jihar Cross River a kudancin Najeriya. [2]

Ya kuma kasance tsohon shugaban KPMG, tsohon shugaban Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria (ICAN). [3] Cif Ani, shi ne shugaban dangi na Mbiabo Ikoneto a jihar Cross River, a yankin Neja Delta a Najeriya. Ya kasance akawun aiki wanda Janar Sani Abacha ya naɗa a matsayin ƙaramin ministan harkokin waje a cikin shekarar 1993, sannan kuma aka naɗa shi ministan Kuɗi a cikin shekarar 1994.

  1. Privatisation process is riddled with corruption –Ani http://theeconomyng.com/?p=196
  2. Former finance minister lauds FG's agricultural diversification programme http://thenationonlineng.net/former-finance-minister-lauds-fgs-agricultural-diversification-programme/
  3. ANI: Increase In VAT, Devaluation Of Naira And Fuel Subsidy Removal Are Not Fundamental To Revamping Economy https://m.guardian.ng/business-services/ani-increase-in-vat-devaluation-of-naira-and-fuel-subsidy-removal-are-not-fundamental-to-revamping-economy/