Jump to content

Asibitin ƙashi na ƙasa na Igbobi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Asibitin ƙashi na ƙasa na Igbobi
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaLagos
BirniLagos
Coordinates 6°31′52″N 3°22′13″E / 6.53123016°N 3.37018389°E / 6.53123016; 3.37018389
Map
History and use
Opening1945
Offical website

Asibitin ƙashi na ƙasa na Igbobi, asibiti ne a Legas, Najeriya. [1] Har ila yau, ana kiransa da sunan “igbobi” ko “asibitin igbobi”.

A cikin shekarar 2019, asibitin ya haɗu da SIGN Fracture Care International, Amurka don magance naƙasar hannu. [2]

Asibitin Orthopedic na ƙasa, na Igbobi, Legas ya fara aiki a matsayin cibiyar farfaɗo da sojojin da suka samu raunuka a yakin duniya na biyu a shekarar 1943, daga nan kuma ta ci gaba da zama asibiti ƙarƙashin kulawar likitocin Turawan mulkin mallaka na Burtaniya na Turawan mulkin mallaka na Najeriya a ranar 6 ga watan Disamba 1945. Asibitin wanda aka fara kiransa da Royal Orthopedic Hospital a shekarar 1956 ya kuma taka rawar gani wajen jinyar da sojoji da fararen hula da suka jikkata a yakin basasar Najeriya na shekarun 1967-1970. An mika asibitin ga gwamnatin jihar Legas a shekarar 1975 sannan kuma gwamnatin tarayya a shekarar 1979.[3][4][5]

Kiwon lafiya

[gyara sashe | gyara masomin]

Asibitin tana da ƙarfin ma'aikata kusan 1300. Tana da rukunin kulawa mai zurfi da iya aiki mai gadaje 450. Yanzu ana kyautata zaton asibitin a matsayin babban asibitin kashi a yammacin Afirka. Bankin Mobolaji Anthony ya ɗauki nauyin wani sabon sashe na asibitin wanda ya haɗa da gyaran sashen gaggawa.[3][5][6]

Asibitin yana da waɗannan sassan da aka jera don biyan buƙatun marasa lafiya [7]

Karamin Ministan Lafiya na lokacin, Dr Olorunnibe Mamora ne ya kaddamar da ɗakin jin daɗi da ke NOHIL wanda shi ne ɓangare mai zaman kansa na asibitin a ranar 1 ga watan Afrilu, 2021. An gina shi da kayan aiki na musamman don kulawa mai ƙima. Haka kuma a wannan rana, Modular Theatre mai suites shida an kuma kaddamar da aikin. [8]

A cikin shekarar 2022, an buɗe ɗakin gwaje-gwaje na kwayoyin halitta na zamani a asibiti don magance cututtuka kamar COVID'19 da yin gwaje-gwaje kamar PCR. [9]

  1. Edema, Grace (2022-08-16). "NOHIL unveils molecular laboratory". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-01-21.
  2. "National Orthopaedic Hospital Igbobi, partners experts on limb deformity". Vanguard. Retrieved 14 November 2023.
  3. 3.0 3.1 "National Orthopaedic Hospital Opens Skills Laboratory in Lagos". Channels Television. Retrieved 21 January 2016.
  4. Popoola Babalola (15 December 2015). "NBTE accredits Orthopaedic Hospital's college …as 96 nurses, health assistants graduate". The Vanguard.
  5. 5.0 5.1 Joseph Okoghenun (24 December 2015). "Igbobi hospital seeks improvement in health insurance, services". Nigerian Guardian. Retrieved 21 January 2016.
  6. "My challenges at Igbobi Orthopaedic hospital, by new MD". The Nation. 2 December 2008. Retrieved 21 January 2016.
  7. "News-NOHIL Management Board Commissions New Molecular Laboratory". www.nohlagos.gov.ng. Retrieved 2022-12-28.
  8. Obinna, Chioma (April 6, 2021). "Healthcare: FG building healthy system accessible to all, says Mamora". Vanguard. Retrieved November 14, 2023.
  9. Edema, Grace (2022-08-16). "NOHIL unveils molecular laboratory". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-01-21.