Atika bint Yazid

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Atika bint Yazid
Rayuwa
Mutuwa 8 century
Ƴan uwa
Mahaifi Yazid I
Abokiyar zama Abd al-Malik ibn Marwan (en) Fassara
Yara
Ahali Muawiya II (en) Fassara, Khalid ibn Yazid (en) Fassara da Abd Allah ibn Yazid (en) Fassara
Sana'a
Sana'a marubuci

Ātika bint Yazid ( Larabci: عاتكة بنت يزيد‎ ) Gimbiyar Banu Umayya ce. Ita ce 'yar Yazid I, kuma matar Abdul-Malik bn Marwan. Wasu suna kiranta da shedar karatun addinin musulunci musamman Hadisi. Ana kuma kiranta da kyauta yayin da tabada duk kuɗinta ga wani matalauci daga cikin dangin Abu Sufyan.

Rayuwarta[gyara sashe | gyara masomin]

Atika diya ce ga khalifan Umayyawa na biyu Yazid. Ita ce kanwar khalifan Umayyawa na uku Mu'awiya II. Kafin Yazid I ya rasu, yasa aka yi wa dansa bay’ah. Mu'awiya na biyu ya gaji mahaifinsa a Damascus a shekara ta 64 bayan hijira (Nuwamba 683 miladiyya), yana ɗan shekara sha bakwai 17 a duniya. Dan uwanta ya rasu a shekara ta 684, kuma surukinta Marwan ne ya gaje shi, yayi mulki na tsawon shekara daya ya rasu a shekara ta 685. Marwan ya kasance mijinta, Abd al-Malik ya gajeshi a matsayin khalifan Umayyawa na biyar. Ita ce babbar matar Abd al-Malik, babban danta shi ne aka zaba magajin khalifanci.

Ta hanyar zuriyarsa, danta Yazid ya kasance dan takara na dabi'a don maye gurbin khalifanci. [1] Wata zuriyar Larabawa mai daraja ta uwa ta kasance tana da nauyin siyasa a wannan lokaci a tarihin khalifanci, [2] kuma Yazid ya yi alfahari da zuriyarsa ta Sufyani, yana ganin ya fi 'yan uwansa Marwanid. [2] An zabeshi ta wurin ƙanin mahaifinsa, Khalifa Sulaiman ( r. 715–717 ) a matsayin na biyu a jerin khalifanci bayan dan uwansu na farko Umar II, wanda ya yi mulki daga shekarar 717 zuwa [1] 720 [1] [3] Zuriyar Yazid II ta haɗa reshen mahaifinsa Marwanid na daular Umayyawa, a kan mulki tun shekara ta 684, da kuma reshen Sufyani na Yazid I da mahaifansu na ƙarshe Mu'awiya I ( r. 661–680 ), wanda ya kafa Khalifancin Umayyawa. [1]

Atika da Abd al-Malik sun haifi 'ya'ya maza; Yazid II, Marwan al-Asghar, Mu'awiya da wata mace, Umm Kulthum. [4] [5] daga aurensu.

Duk da haka, ansan Atika da cewa ta kasance dangi ga khalifofi Umayyawa goma sha biyu daga cikin goma sha hudu [lower-alpha 1] . Hakan yasa ta cire Hijabinta a gabansu. Babu wata mace da aka sani da tana da irin wannan adadin muharramai tsakanin khalifofi.

Ta tsira daga mutuwar jikanta Al Walid II.

Khalifofi masu alaka da ita[gyara sashe | gyara masomin]

Khalifofin da suke da alaka da ita sune:

A'a. Halifa Dangantaka
1 Mu'awiya I Kaka
2 Yazid I Uba
3 Mu'awiya II Dan uwa
4 Marwan I Suruki
5 Abdul Malik Miji
6 Al-Walid I 'Ya'yan maza
7 Sulaiman [5]
9 Yazid II [1] Son
10 Hisham Dan uwa
11 Al-Walid II Jikan
12 Yazid III Jikoki-jikoki
13 Ibrahim bin Walid

Bayanan kula[gyara sashe | gyara masomin]

  1. The other two were Umar II, and Marwan II, nephews of her husband

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Lammens & Blankinship 2002.
  2. 2.0 2.1 Wellhausen 1927.
  3. Powers 1989.
  4. Ahmed 2010.
  5. 5.0 5.1 Hinds 1990.

Littafai Masu Tsarki[gyara sashe | gyara masomin]

  •  
  •  
  •  
  •  
  •