Azman Air
![]() | |
---|---|
AZM | |
![]() | |
Bayanai | |
Iri | kamfanin zirga-zirgar jirgin sama |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Mulki | |
Hedkwata | Kano |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2010 |
airazman.com |
Azman Air Services Limited kamfanin zirga-zirgar jirgin sama ne mai mazauni a birnin Kano na Najeriya. An kafa kamfanin a shekarar 2010 mallakin dan kasuwa Abdulmunaf Yunusa Sarina, kamfanin na jigilar fasinjojin sa daga mazaunin wato Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, a birnin Kano. An kaddamar da kamfanin Azman Air a 2010 amma sai a 2014 ya fara aiyukan sa da jigilar sa ta farko da yayi zuwa filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe daga Kano ranar 16 ga Mayu 2014. Azman ya fara jigilar sa a Najeriya da jirage 2 Boeing 737-500.