Babban Masallacin Dubai
Babban Masallacin Dubai | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Taraiyar larabawa |
Haɗaɗɗiyar daular larabawa | Dubai |
Birni | Dubai (birni) |
Coordinates | 25°15′52″N 55°17′48″E / 25.2644°N 55.2967°E |
History and use | |
Opening | 1900 |
|
Masallacin Harami ( Larabci: مسجد دبي الكبير ) wani masallaci ne a birnin Dubai, Masarautar Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa. Yana tsakanin, textile souk, da gidan kayan tarihi na Dubai kusa da wani ƙaramin rafi a yankin Bur Dubai. Asali an gina shi a shekarar 1900, aka ruguje shi aka sake ginawa a shekarar 1960, sannan aka sake yin ginin a shekar 1998 (ginin da yake yanzu). Yanzu yana iya ɗaukar masu *Wikimedia Awareness in Kwami*
Dive into the Wikimedia Awareness in Kwami project, a month-long initiative designed to empower contributors for Wikimedia Foundation projects. From January 28 to February 28, 2023, engage in the Edit-a-thon for hands-on learning and the chance to win exclusive *vouchers.* Stay tuned for the exciting voucher awards unveiling. Your valuable contributions matter, and we invite you to be a part of this enriching experience. Visit the metapage at https://meta.m.wikimedia.org/wiki/Event:Wikimedia_Awareness_in_Kwami for comprehensive details. Seize this opportunity to enhance your skills and leave your mark on Wikimedia projects. Join us on this collaborative journey!ibada har mutum 1,200. An ba wa waɗanda ba Musulmi ba damar shiga Masallacin a kullum daga ranar Lahadi zuwa Alhamis daga karfe 9 na safe zuwa 11:30 na safe don yawon buɗe ido kyauta.[1][2] Masallacin shi ne cibiyar harkokin addini da al'adun Dubai.[3]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Asalin masallacin makaranta ce da aka sadaukar domin karatun kur'ani mai suna kuttab, wacce ta yi maraba da ɗalibanta na farko a shekara ta 1900 don koyon Alkur'ani mai girma.[2] An maye gurbin wannan ginin da sabon masallacin da ke wannan wuri a shekarar 1960, wanda kuma shi kansa aka sake gina shi a shekarar 1998, kusa da na asali na 1900.[1][4] Wannan masallaci na ɗaya daga cikin masallaci mafiya girma a Dubai kuma shi ne babban gini a tsohon birnin.[1]
Gine-gine
[gyara sashe | gyara masomin]Mafi girman fasalin masallacin shine tsawon mita 70 metres (230 ft) na minaret, mafi tsayi a Dubai, wanda yayi kama da wani gini mai suna lighthouse. Bangon mai ƙunshe da yashi-launin toka gabaɗaya ba a yi musu ado ba, amma akwai wani rubutun Alqur'ani da aka jera a sama da ginshiƙai biyar na fuskar ƙofar, wanda ke zaune a saman ɗan gajeren jirgi mai matakai shida.[1][4] Kananan hasumiyoyi 45 da wasu kwara 9 manya masu tsayi, sun rufe rufin babban Masallacin Harami.[1] An saka tagogin katako da gilashin da aka yi da hannu tare da haɗawa da tsohon garin Bur Dubai, kuma hasumiyar an tsara ta da tsarin gine-ginen Anatolia. An shawarci maziyartan masallacin da su sanya tufafin da suka dace (kafin kai ziyara).[2] Masallacin yana ɗaukar masu ibada har 1,200 alokaci ɗaya.[5] Tashar metro, Al Fahidi itace tasha mafi kusa da babban masallacin.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Masallacin Jumeirah
- Musulunci a Hadaddiyar Daular Larabawa
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 Thomas,Gavin (3 September 2009). Frommer's Dubai and Abu Dhabi Day by Day. John Wiley & Sons. pp. 41–42. ISBN 978-0-470-68459-7.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Lyons, Colette (December 8, 2010). The Unofficial Guide to Dubai. John Wiley & Sons. p. 187.
- ↑ "Lonely Planet review for Grand Mosque". Lonely Planet. Retrieved 1 June 2013.
- ↑ 4.0 4.1 Thomas, Gavin (September 3, 2009). Frommer's Dubai and Abu Dhabi Day by Day. p. 41.
- ↑ Ian Cross; Pilot Productions (2005). Adventure Golf: From Fairways to Fun Days Attractions on and Off the World's Most Remarkable Golf Courses. GLOBE PEQUOT Press. p. 107. ISBN 978-0-7627-3790-1.