Baiko
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
promise (en) ![]() ![]() |
Mabiyi |
courtship (en) ![]() |
Ta biyo baya | Aure |
Yana haddasa |
fiancé (en) ![]() |
Hannun riga da |
disengagement (en) ![]() |
Baiko wani biki ne na yarjejeniya akan amincewa da neman aure tsakanin namiji da mace.[1] A kasar Hausa kuwa, baiko wata al'ada ce wacce ake yi gabanin aure. Ana baiko ne a lokacin da Budurwa da saurayi suka amince da cewa zasu zauna da juna a matsayin ma'aurata. To a wannan lokacin ne za'a dakatar da duk wani saurayi dake nemanta (da aure) saboda cewa an amince za'a aurar da ita ne ga wanda ta zaba daga cikin samarinta. Daga nan dangin ango zasu kawo wasu kudi wanda ake kira da kudin baiko ko kudin sa rana tare da shaidu daga ɓangaren amarya da na ango Bayan anyi baiko sai kuma shirye-shiryen daurin aure.