Jump to content

Bank PHB

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bank PHB
Bayanai
Suna a hukumance
commercial bank in Nigeria
Iri kamfani
Masana'anta economics of banking (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Aiki
Ƙaramar kamfani na
Harshen amfani Turanci
Kayayyaki
loan (en) Fassara
Mulki
Hedkwata Lagos,
Mamallaki Bank PHB
Tarihi
Ƙirƙira 2005
Dissolved 5 ga Augusta, 2011
bankphb.com

Bankin PHB, wanda aka fi sani da Platinum Habib Bank, bankin kasuwanci ne a Najeriya. Bankin ya kasance na biyar a girma a wajen samar da hada-hadan kuɗi a Najeriya. [1] An kiyasta kadarorin bankin sun haura dalar Amurka biliyan 6. [2]

Manyan Jami'ai

Francis Atuche- Shugaba/MD na Bankin PHB [3]

Bank PHB Group

[gyara sashe | gyara masomin]

Bank PHB memba ne na Bankin PHB Group, wacce ke da hedkwata a Lagos, Najeriya, tare da rassa a Gambia, Laberiya, Najeriya, Saliyo da Uganda.

An kafa bankin PHB ne a shekarar 2005 ta hanyar hadakar bankin Platinum Plc da Habib Nigeria Bank Plc . Tun lokacin da aka kafa bankin, bankin ya bi dabarun faɗaɗa shi ta hanyar saye da samar da rassa a ciki da wajen kasarsa ta Najeriya. (Duba Rukunin PHB Bank ).

Kasawa da rufewa

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 5 ga watan Agusta, 2011, babban bankin Najeriya ya soke lasisin aiki na BankPHB tare da na Afribank da Spring Bank saboda ba su nuna iyawa da ikon dawo da jarin su ba kafin ranar 30 ga watan Satumba, 2011 na mayar da jari.

An ƙirƙira Bankin Keystone ne a ranar 5 ga watan Agusta, 2011, ta hanyar karɓar duk kadarorin (ciki har da rassa) da kuma basukan bankin PHB wanda babu shi a yanzu, wanda aka soke lasisinsa na harkokin kasuwancin banki a wannan rana.

Duba kuma 

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. Bank PHB is 5th Largest Bank in Nigeria[permanent dead link]
  2. Bank PHB Financials 2008[permanent dead link]
  3. Empty citation (help)About Keystone Bank Limited. Keystone Bank. Retrieved on August 29, 2014.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]