Jump to content

Benazir Bhutto

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Benazir Bhutto
Leader of the Opposition (en) Fassara

17 ga Faburairu, 1997 - 12 Oktoba 1999
Nawaz Sharif (en) Fassara - Fazal-ur-Rehman (en) Fassara
Finance Minister of Pakistan (en) Fassara

26 ga Janairu, 1994 - 10 Oktoba 1996
Firimiyan Indiya

19 Oktoba 1993 - 5 Nuwamba, 1996
Moeenuddin Ahmad Qureshi (en) Fassara - Malik Meraj Khalid (en) Fassara
Leader of the Opposition (en) Fassara

6 Nuwamba, 1990 - 18 ga Afirilu, 1993
Khan Abdul Wali Khan (en) Fassara - Nawaz Sharif (en) Fassara
Defence Minister of Pakistan (en) Fassara

4 Disamba 1988 - 6 ga Augusta, 1990
Firimiyan Indiya

2 Disamba 1988 - 6 ga Augusta, 1990
Muhammad Junejo (en) Fassara - Ghulam Mustafa Jatoi (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Karachi, 21 ga Yuni, 1953
ƙasa Pakistan
Mutuwa Rawalpindi (en) Fassara, 27 Disamba 2007
Makwanci Mausoleum of Zulfikar Ali Bhutto (en) Fassara
Yanayin mutuwa kisan kai (harin ta'addanci)
Ƴan uwa
Mahaifi Zulfiqar Ali Bhutto
Mahaifiya Nusrat Bhutto
Abokiyar zama Asif Ali Zardari (en) Fassara
Yara
Ahali Sanam Bhutto (en) Fassara, Shahnawaz Bhutto (en) Fassara da Murtaza Bhutto (en) Fassara
Yare Bhutto family (en) Fassara
Karatu
Makaranta Radcliffe College (en) Fassara
Karachi Grammar School (en) Fassara
Convent of Jesus and Mary, Murree (en) Fassara
Presentation Convent Girls High School (en) Fassara
Convent of Jesus and Mary, Karachi (en) Fassara
Jami'ar Harvard
St Catherine's College (en) Fassara
Lady Margaret Hall (en) Fassara
Eliot House (en) Fassara
Matakin karatu Doctor of Sciences (en) Fassara
Harsuna Urdu
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Kyaututtuka
Mamba Phi Beta Kappa Society (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Pakistan Peoples Party (en) Fassara
IMDb nm1567097
benazirbhutto.com

Benazir Bhutto (An haifeta ranar 21 ga watan Yuni, 1953) a birnin Karachi, dake ƙasar Pakistan. `Yar siyasace.

Farkon rauywa da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Benazir Bhutto ta soma karatu a makarantar Nursery ta Lady Jennings da ke Karachi. Bayan shekaru biyu sai ta sami shiga makarantar Firamare ta Mary Convent da ke Muree, in da ta kammala karantunta na Firamare tattare da sakamako mai kyau.

Bayan ta kammala karatun gaba da Firamare, a watan Afirilu na shekarar 1969, Bhutto ta shiga jami'ar Havert da ke ƙasar Amurka, in da ta kammala karatun Jami'a a watan Yuni na 1973, tare da samun digiri na farko a fannin ilimin kimiyyar siyasa, da tattali.

A shekarar 1976, Benazir Bhutto ta koma cigaba da karatu a jami'ar Oxford da ke London don neman babbar digiri. Ta kammala karatun in da ta koma Pakistan cikin watan Yuni na shekara 1977

Soma Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Benazir Bhutto

Kodayake dai bayan kammala karatunta, Benazir Bhutto ta so ta yi aiki a ƙetare, to amma mahaifin ta ya nemi ta komo gida ta shiga siyasa domin ta tsaya takarar kujerar majalisar dokoki, sai dai kuma kash, shekarun Bhutto ba su kai na tsayawa takarar shiga majalisar ƙasa ba, don haka ne mahaifin Bhutto Zulfikar Ali Bhutto, ya umurce ta da ta taimaka masa wajen tafiyar da harkokin siyasa. An zaɓi mahaifin Bhutto a muƙamin Firaminista, to amma kuma a yayin da ta koma gida Pakistan don taimakawa mahaifinta ne sojoji suka yi masa juyin mulki.

Hukunci da daurin talala[gyara sashe | gyara masomin]

Hukuncin kisa ga mahaifinta[gyara sashe | gyara masomin]

Gwamnatin Janar Zia Ul Haq, ta zartas da hukuncin kisa kan mahaifin Bhutto a cikin shekarar 1979,

ɗaurin talala[gyara sashe | gyara masomin]

Sa'anan akayi wa Bhutto ɗaurin talala na shekaru uku. A shekarar 1984, anyi wa Bhutto izinin barin Pakistan, don haka ta je tayi zaman ta a London tare da yan'uwanta su biyu. Benazir Bhutto ta koma Pakistan domin ta halarci taron jana'izar ɗan'uwanta wanda ya rasu a shekarar 1985, to sai dai gwamnatin Pakistan ta kuma kame ta bayan ta zarge ta da lefin shiga zanga-zangar nuna ƙyamar gwamnati.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Rawar gani[gyara sashe | gyara masomin]

Benazir Bhutto

Benazir Bhutto a bisani ta kasance mai taka rawar gani cikin jami'iyyar (PPP), wato jamaiyyar mahaifinta. Kodayake ba ta iya zama cikin ƙasar Pakistan ba, to amma tana bada gudummawa gaya ga jama'iyyar ta( PPP) kafin kuma a bisani ta zama shuagabar jamia'iyyar, in da ta gaji mahaifinta, lokacin da ta koma gida Pakistan bayan mutuwar shugaba Janar Muhammad Zia-ul-Haq. Wannan ne ma ya baiwa jama'iyyar Bhutto ta “Pakistan People Party”, damar lashe zaɓen majalisar dokokin ƙasar da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwambar 1988, sa'annan kuma aka rantsar da ita a muƙamin Firaminista a gwamnatin haɗin gambiza a ranar 2, ga watan Disambar 1988. Wannan ne ma ya sa Bhutto ta shiga tarihin ƙasar a matsayin mace ta farko kuma mafi ƙarancin shekaru da ta hau muƙamin Firaminista a Pakistan, don kuwa duka-duka shekarunta 35 ne da haihuwa a lokacin.

Juyin mulki[gyara sashe | gyara masomin]

An kifar da gwamnatin Bhutto a 1990, in da Nawaz Sharif ya hau muƙamin Firaminista, to amma an kuma zaɓen ta a shekarar 1993, duk da hakan ba ta kai labari ba, don kuwa shugaba Farooq Leghari, ya zargi gwamnatin Bhutto da lefin rashawa. Bayan hamɓarar da gwamnatin Bhutto, a bisani ta fuskanci zarge-zarge da dama, mussaman kan yadda aka ce tana baiwa gwamnatin taliban a ƙasar Afghanistan goyon baya, don haka ne ma ƙasashen duniya irin su Faransa da Andalus wato Spain, da Swizaland, suka zargi Bhutto da laifin aikata laifufuka daban-daban a ƙasashen su da suka shafi na hada-hadar ƙudi, to amma jama'iyyarta ta (PPP) ta fito fili ta ƙaryata zarge-zargen.

Benazir Bhutto

A shekara ta 2002, shugaban Pakistan Pervez Musharraf, ya yi wa kundin tsarin mulkin Pakistan gyara, wanda hakan ya hamarta wa duk wani daya riƙe muƙamin Firaminista hawa mulki fiye da sau biyu, wanda hakan ya zama wata katangar da ta yi haramci ga Bhutto neman muƙamin Firamnista. A ranar uku, ga watan Agustan 2003, an zaɓi Benazir Bhutto, mamba cikin cibiyar Miinhaj ul-Quran ta duniya. Ta ci gaba da kasancewa a cibiyar har zuwa 2004, lokacin da ta koma Dubai da ke tarayar Daular Larabawa , in da ta ci gaba da zama tare da iyalanta, da suka haɗa da ‘ya'yanta uku, da mijinta, da kuma sauran iyalan ta. Benazir Bhutto ta bayyana aniyarta ta komawa Pakistan a shekara ta 2007, domin shiga siyasa gadan-gadan, kodayake shugaba Musharraf ya yi barazanar cewa zai haramta mata damar tsayawa takara, to amma kuma a bisani an yaɗa raɗe-raɗin cewar wata ƙil gwamnatin Musharraf ce ta kuma baiwa Bhutto damar komawa siyasa bayan wata ganawar da suka yi da ita a shekara ta 2004 .

Mafaka[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan tayi zama na neman mafakar siyasa na kimanin shekaru takwas a tsakanin Dubai da London, Benazir Bhutto ta koma ƙasar Pakistan a ranar 18 ga watan Oktoba na shekara ta 2007, don sake komawa fagen siyasa da zummarta ta tsayawa takara a babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2008. To sai dai kuma a kan hanyarta ta komawa birnin Karachi a ranar 18 ga watan Oktoba na shekara ta 2007, Bhutto ta fuskanci hare-haren boma-bomai har saw biyu, da suka fashe jim kaɗan bayan ta baro babban filin saukar jiragen sama na Jennah. Du da cewar Bhutto bata sami koda ƙwarzani ba daga hare haren, to amma aƙalla magoya bayan ta su 136, ne suka mutu, sa'anan wasu 450, suka sami munanan raunuka, cikin waɗanda suka mutu akwai wasu Mutane 50, waɗanda suka yi kamun hannu na zobe, don kare Bhutto daga hare-haren ƙunar baƙin wake.

Allah wadai[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar uku, ga watan Nuwambar shekara ta 2007, Shugaban Pakistan Pervez Musharraf, ya sanar da kafa dokar ta ɓaci a kan dalilan rashin cikkaken tsaro a ƙasar, kana kuma ya sauke babban Jojin ƙasar ya naɗa wani, tare kuma da kamewa da kuma tsare wasu dake adawa da gwamnatinsa. Bhutto ta yi Allah wadai da wannan manufa ta Musharraf don haka ne ma aka soma fuskantar sa-in-sa tsakanin Bhutto da gwamnatin Musharraf, lamarin da ya kai ga yi wa Benazir Bhutto ɗaurin talala a ranar 8, ga watan Nuwamba, kwanaki biyar bayan kafa dokar ta ɓaci. Bayan anyi ta gwa-gwa-gwa, a bisani dai Musharraf ya sako ta, don haka ne ma ta sami zarafin shigar da takardarta ta neman tsayawa takarar zaɓe na ‘yar majalisa daga mazaɓar Larkana, a ranar 24, ga watan Nuwambar 2007.

Hari[gyara sashe | gyara masomin]

Benazir Bhutto

Shugaba Musharraf ya sauka daga kan muƙamin shugaban mulkin soja, sannan ya kuma ɗaukar rantsuwa a muƙamin shugaban farar hula a ranar 30, ga watan Nuwamba, 2007. Kana ya cire dokar ta baci a ranar 16, ga watan Dizambar shekarar, biye da kudirin yin zaɓe a watan Janairu na 2008. A ranar takwas ga watan Disamba na 2007, wasu ‘yan bindiga su uku, sun kutsa kai ofishin jama'iyyar Bhutto dake kudu maso yammacin lardin Baluchistan, in da suka kashe magoya bayan Benazir Bhutto su uku.

Dalilin mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Benazir Bhutto, ta gamu da sanadin ajalin ta ne dai a ranar 27 ga watan Disambar shekara ta 2007, bayan wani ya harbe ta da bindiga kafin a bisani ya ta da bom da ya hallaka shi, a yayin da Bhutto ke ƙoƙarin fita daga harabar data gudanar da wani gangami na jama'iyyarta ta (PPP) a garin Rawalpindi.

Benazir Bhutto

An ce aƙalla Mutane 22 suka mutu a wannan hari, wasu da dama suka sami raunuka. An sanar da mutuwar Bhutto ne dai a bayan an kai ta babban Asibitin Rawalpindi, in da Allah ya yi mata cikawa, kuma an sanar wa duniya rasuwarta da misalin ƙarfe 6, da minti 16, na rana agogon Pakistan, ko kuma ƙarfe 2 da miniti 16, agogon Nigeriya da Niger. Ƙasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da kashe Bhutto, in da wasu ke ɗora laifin harin kan gwamnatin Musharraf, zargin da shugaba Musharraf ya ƙaryata.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]