Bill Gates
Bill Gates (an haifeshi ranar 28 ga watan Oktoban, shekarar 1955), kuma ya tashi a Seattle, Gates sun kirkiro 'Microsoft' tare da abokinsa Paul Allen a shekara ta (1975), a Albuquerque, 'New Mexico'Sun zama babban kampanin komputa a duniya. Bill Gates ya jagoranci kampanin a matsayin CEO har lokacin da ya sauka a matsayin, a watan Janairu a shekara ta (2000), sannan shugaban software architect. A karshen shekarun (1990) . An zarge shi da zamba a kasuwanci , wanda ake cewa adawar kasuwanci ce kawai. An dauke hakan a kotuna da yawa. A watan yuni a shekara ta (2006), Bill Gates [1] ya sanar da cewa zai karkatar da rabin aikin sa a Microsoft da cikakken aikinsa zuwa Bill & Melinda Gates Foundation , wato gidauniyar su ta sirri wadda da shi da matar sa, Melinda Gates , suka kirkira a shekarar( 2000). A sannu a hankali ya mika aikin sa ga
Ray Ozzid da Craig Mundie . Yayi murabus daga matsayin shugaban Microsoft a watan Fewarun a shekara ta ( 2014), sannan ya koma a matsayin me bada shawara don taimakawa sabon shugaban wato Satya Nadella. A watan maris a shekara ta ( 2020) , Bill Gates ya bar makamin sa a Microsoft da Berkshire Hathawadon ya maida hankali a kan ayyukan sa na taimako, wadda ya kunshi chanjin yanayi, Lapiyar duniya da ci gaba ta da kuma ilimi.
Tun a shekara ta (1987), ya kasance a cikin masu kudin duniya. daga shekara ta (1995 zuwa 2017)[2]
Ya rike matsayin mai kudin duniya har shekaru hudu. watan octoba a shekara ta( 2017) , CEO Jeff mawallafin Amazon ya zo ya kere shi kudi wanda kimanin kudin sa suka kai dalar amrika dala biliyan ($90.6), shi kuma Bill Gates yanada( $89.9). A watan nuwamba a shekara ta (2020), Bill Gates ya mallaki kimanin kudi dala biliyan ($113.7) lokacin. A watan nuwamba a shekarar (2020), Bill Gates wadda ya koma bayan Bezos da Elon Musk wato mataki na uku na masu kudin duniya.