Bill gate
An haife shi kuma ya tashi a Seattle, Gates sun kirkiro Microsoft tare da abokin sa Paul Allen a 1975, a Albuquerque, New Mexico ;Sun zama babban kampanin komputa a duniya. Gates ya jagoranci kampanin a matsayin CEO har lokacin da ya sauka a matsayin, a watan Janairu 2000, sannan shugaban software architect. A karshen shekarun 1990s. An zarge shi da zamba a kasuwanci , wanda ake cewa adawar kasuwanci ce kawai .An dauke hakan a kotuna da yawa. A watan yuni 2006, Gates ya sanar da cewa zai karkatar da rabin aikin sa a Microsoft da cikakken aiki sa zuwa Bill & Melinda Gates Foundation , wato gidauniyar su ta sirri wadda da shi da matar sa, Melinda Gates , suka kirkira a shekara 2000. A sannu a hankali ya mika aikin sa ga
Ray Ozzid da Craig Mundie . Yayi murabus daga matsayin shugaban Microsoft a watan fabrairu 2014 sannan ya koma a matsayin me bada shawara don taimakawa sabon shugaban wato Satya Nadella .A watan maris 2020, Gate ya bar makamin sa a Microsoft da Berkshire Hathawadon ya maida hankali a kan ayyukan sa na taimako, wadda ya kunshi chanjin yanayi, Lapiyar duniya da ci gaba ta da kuma ilimi.
Tun a shekara ta 1987 ya kasance a cikin masu kudin duniya. daga 1995 zuwa 2017
Ya rike matsayin me kudin duniya har shekaru hudu. watan octoba a shekara ta 2017, CEO Jeff mawallafin Amazon ya zo ya kere shi kudi wanda kimanin kudin sa suka kai dalar amrika dala biliyan $90.6 shi kuma Gate na da $89.9. A watan nuwamba 2020 Gate ya mallaki kimanin kudi dala biliyan $113.7 lokacin.A watan nuwamba 2020, Gates wadda ya koma bayan Bezos da Elon Musk wato mataki na uku na masu kudin duniya.