Busari Adelakun

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Busari Adelakun
Rayuwa
Haihuwa Ibadan
ƙasa Najeriya
Mutuwa Lagos University Teaching Hospital, 1984
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Ibadan Peoples Party (en) Fassara

Busari Adelakun ɗan siyasar Najeriya ne daga yankin Ejioku a Ibadan, jihar Oyo. Ya kasance yana da alaƙa da Action Group da Unity Party of Nigeria (UPN) a jamhuriya ta ɗaya da ta biyu. A matsayinsa na ɗan jam’iyyar UPN da kuma jam’iyyar NPN a Ibadan a jamhuriya ta biyu, Adelakun ya kasance jigo a cikin ruɗanin siyasar birnin.

Tarihin Rayuwarsa[gyara sashe | gyara masomin]

Mahaifin Adelakun manomin koko ne daga Ibadan kuma ya gaji gonar mahaifinsa bayan rasuwar marigayin. Lokacin da ya fara harkokin siyasa na farko, shi ne ya wakilci mahaifinsa a lokacin taron jam'iyyar Ibadan Peoples Party. Daga nan ne Adelakun ya shiga ƙungiyar Action Group, aiki ne mai wahala jam’iyyar ta samu goyon baya a Ibadan saboda farin jinin mutum ɗaya mai suna Adegoke Adelabu, ko da bayan rasuwar Adelabu AG bai samu goyon baya sosai a Ibadan da tashin hankalin da ya ɓarke. bayan mutuwar Adelabu ya auka wa da yawa daga cikin ƴaƴan jam’iyyar. An samu saɓani a AG tsakanin Firimiyan yankin, Akintola da tsohon Firimiya, Awolowo a shekarar 1962. Adelakun ya goyi bayan ɓangaren Awolowo. Daga nan kuma sai ɓangaren Adelakun ya yi rauni a Ibadan a lokacin da rikici ya ɓarke a yankin Yamma. Bayan juyin mulkin soji ya rusa jamhuriyar dimokuraɗiyyar, Adelakun ya koma noma, ya kuma shiga ƙungiyar manoma, ya zama shugaban ƙungiyar.

A shekarar 1976, ya lashe zaɓen ƙananan hukumomi a Ibadan bayan wasu ƴan koma-baya da suka haɗa da hana shi takara da farko. Bayan da aka hana shi takara da farko, magoya bayan Adelakun sun ƙauracewa zaɓen, yayin da ya garzaya kotu ya bayyana cewa zaɓen ba shi da tushe. Kotun ta amince da buƙatarsa kuma bayan an gudanar da sabon zaɓen ne aka bayyana Adelakun a matsayin wanda ya lashe zaɓen. A shekarar 1979, Adelakun ya haɗa kai da wani shugaban jam’iyyar, Archdeacon Emmanuel Alayande, domin taimakawa jam’iyyar UPN ta samu rinjayen ƙuri’u a Ibadan, wannan shi ne karon farko da jam’iyyar Awolowo ta samu rinjayen ƙuri’u a birnin. A shekarar 1979 aka naɗa shi kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar Oyo, bayan shekaru biyu, sai aka mayar da shi ma’aikatar lafiya.

A shekarar 1983, Adelakun ya shiga ɓangaren da ke adawa da takarar Bola Ige a matsayin gwamnan UPN. Daga baya Adelakun da wani ɗan jam’iyyar Sunday Afolabi sun koma jam’iyyar adawa ta NPN

An ɗaure Adelakun a gidan yari a shekarar 1984 a hannun wani sabon shugaban sojoji ƙarƙashin Manjo-Janar Muhammadu Buhari.[1]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Legas sakamakon rashin lafiya da yake fama da shi a lokacin da yake tsare a gidan yari.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Bawa, FFK, Shehu: Of slump, slum and somersault". TheCable. 2021-09-18. Retrieved 2022-08-11.
  2. https://www.thecable.ng/bawa-ffk-shehu-of-slump-slum-and-somersault