Jump to content

Christopher Odetunde

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Christopher Odetunde
Rayuwa
Haihuwa Kwara, 
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Embry–Riddle Aeronautical University, Daytona Beach (en) Fassara
Iowa State University (en) Fassara
Texas A&M University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami

Christopher Odetunde, farfesa ne a fannin injiniyan jiragen sama da Mechanical Engineering. Ya riƙe muƙamai daban-daban a masana'antu da makarantu yayin da yake Amurka da kuma a Najeriya. Shi ne tsohon shugaban tsangayar Injiniyanci a Jami’ar Jihar Kwara, Malete[1] kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Augustine na yanzu.[2]

Odetunde ya yi karatunsa na sakandare a St. John's College Kaduna daga shekarun 1964 zuwa 1968, inda ya karanci fannin fasaha. Canjin sa zuwa fannonin kimiyya ya zo ne a matakinsa na A, wanda ya wuce tsakanin shekarun 1969 zuwa 1972.

Daga nan ya ci gaba da karatun Injiniyanci a fannin Aeronautical a Jami'ar Embry-Riddle Aeronautical dake Amurka. Ya sami wasu digiri a Jami'ar Jihar Iowa, Jami'ar Texas A&M da Cibiyar Fasaha ta Kudu maso Gabas, Alabama. Yana da Digiri na Dakta na Kimiyya a Injiniyancin Aeronautical, Master of science a Injiniyancin Aeronautical/Mechanical da Gudanar da Ayyuka, haka kuma da Digiri na Dakta a fannin Injiniyanci na Aerospace.[3]

Odetunde ya zama Mataimakin Shugaban Jami'ar Augustine a ranar 5 ga watan Oktoba 2020. Har zuwa lokacin da aka naɗa shi, ya kasance tsohon shugaban tsangayar Injiniyanci a Jami’ar Jihar Kwara, Malete.[4][5][6][7]

  1. "Kwara State University – University for Community Development". Archived from the original on 9 December 2022. Retrieved 3 March 2022.
  2. "Augustine University Ilara Epe: History". augustineuniversity.edu.ng.
  3. https://nuc.edu.ng/wp-content/uploads/2019/02/Directory-of-Full-Professors-in-the-Nigerian-University-System.pdf [bare URL PDF]
  4. "VC canvasses holistic education system for national devt". 16 December 2021. Archived from the original on 3 November 2023. Retrieved 31 December 2023.
  5. "Augustine University Ilara Epe:News". augustineuniversity.edu.ng.
  6. "All You Need To Know About Augustine University - Vice Chancellor" via www.youtube.com.
  7. "Igbomina Professor, Bode Odetunde appointed Vice Chancellor in Lagos". 18 September 2020. Archived from the original on 15 August 2022. Retrieved 31 December 2023.