Christy Obekpa
Christy Obekpa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Najeriya, 15 Disamba 1971 (52 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen Ibo |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Harshen Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | judoka (en) |
Christy Obekpa yanzu Mrs Aremu (an haife tana ne a ranar 15 ga watan Disambar 1971), ta kasan ce yar wasan judoka ce ta Najeriya wacce ta shiga gasar ajin mata masu matsakaicin nauyi. Ta lashe lambar tagulla a wasannin Commonwealth Judo na 1990 da lambar azurfa a Gasar Judo ta 1992 CW . Misis Aremu ita ce mace ta farko da ta lashe lambar yabo ta judo Commonwealth. Ta kuma lashe lambobin tagulla biyu a Wasannin Afirka na 1999 da lambar tagulla a Gasar Judo ta Afirka ta 2000.
Aikin wasanni[gyara sashe | gyara masomin]
A cikin 1990, a Gasar Commonwealth Judo da aka gudanar a Auckland, New Zealand . Ta halarci gasar kilo 72 inda ta lashe lambar tagulla. A Gasar Commonwealth Judo ta 1992 da aka gudanar a Cardiff, Wales . Ta kuma halarci kuma ta lashe lambar azurfa a bikin kilo 72.