Jump to content

Cibiyar Shugabannin Al'adu ta Afirka da Mata

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cibiyar Shugabannin Al'adu ta Afirka da Mata
Bayanai
Gajeren suna AQWCLN
Iri network (en) Fassara da ma'aikata
Ƙasa Uganda
Tarihi
Ƙirƙira 1 Satumba 2013
aqwcln.org

Cibiyar Sarauniyoyi da matan nahiyar Afirka ta Nazarin Al'adu ta Afirka (AQWCLN). Cibiya ce ta sadarwa ta shugabannin al'adu mata a duk faɗin nahiyar Afirka wacce ke fafutukan neman bayar da shawarwari don ci gaba da inganta rayuwar mata da 'yan mata a duk fadin nahiyar ta Afirka.

An kafa AQWCLN a watan Satumbar shekarar dubu biyu da goma sha uku 2013 lokacin da fiye da Sarauniya arba'in, sarauniya da sauran shugabannin al'adu mata daga kasashe goma sha shida na Afirka suka hadu a Kampala, Uganda, tare da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka.[1][2] An kafa Cibiyar ne don mayar da martani ga"Harare Call to Action" wadda akayi a shekarar dubu biyu da goma sha biyu 2012 a wani taron da kungiyar sadarwar mata ta nahiyar Afirka wato Global Power Women Network Africa ta shirya, wanda suka nemi kafa cibiyoyin sadarwa masu ma'ana tare da shuwagabannin addini, shuwagabannin gargajiya da kuma shuwagabannin al'adu domin aiwatar da shirye-shirye don karewa da inganta haƙƙunan mata da 'yan mata a cikin Tarayyar Afirka.[2][3] Sarauniya Sylvia Nagindda ta Buganda Kingdom da Sarauniya Best Kemigisa, Sarauniya ta Tooro Kingdom ne suka shirya kaddamarwar.[2][4]

Cibiyar sadarwar tana da surori a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka wadda suka hada da Ghana, Uganda, da Malawi.[5][6]

AQWCLN ta yanke shawarar kawar da munanan ayyukan al'adu, musamman kaciyar 'ya'ya mata da aure yara kanana.[7] Sun yi kira don a saki wadanda aka yi wa satar 'yan matan makarantar Chibok da sauran' yan mata da Boko Haram ta sace.[8][9]

Shahararrun mambobi

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. Empty citation (help)
  2. 2.0 2.1 2.2 "UGANDA: United Nations to Launch the African Queens and Women Cultural Leaders Network". Make Every Woman Count. 30 August 2013. Archived from the original on 22 August 2016. Retrieved 6 August 2016.
  3. Nakaweesi, Dorothy (27 August 2013). "Uganda to host African queens". Daily Monitor. Retrieved 6 August 2016.
  4. Mayanja Nkangi, Jehoash (3 September 2013). "Buganda's Nnaabagereka is Africa's gift". Saturday Vision. Retrieved 6 August 2016.
  5. "President Museveni urges women cultural leaders on poverty fight, and land fragmentation". State House of Uganda. 19 November 2014. Retrieved 6 August 2016.
  6. "UN Women Eastern and Southern Africa Regional Newsletter" (PDF). UN Women. June 2015. Archived from the original (PDF) on 2016-08-20. Retrieved 2016-08-06.
  7. "African Queens declare war on HIV, FGM, early marriages". Saturday Vision. 13 September 2013. Retrieved 6 August 2016.
  8. "The African Queens and Women Cultural Leaders Network call for the immediate release of the Nigerian students". Pathways to go. Archived from the original on 2016-08-15. Retrieved 2016-08-06.
  9. Adjoa Awindor, Nanahemaa (9 May 2014). "African Queens and Women Cultural Leaders Network Call For The Release Of The Over 260 Abducted Nigerian School Girls". Peace FM online. Retrieved 6 August 2016.