Jump to content

Daular Ife

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Daular Ife

Wuri
Hular tarihi da daular ife a gidan tarihi
Taswirar daular ife

Daular Ife ita ce daular farko, a tarihin Yarbawa. An kafa ta ne a yankin kudu, maso yammacin Najeriya a yanzu da kuma gabashin Benin. Daular Ife ta kasance daga shekarar 1200 zuwa 1420. Odùduwà ne ya kafa daular, daular ta zama sananniya saboda nagartattun kayan fasaha. Duk da cewa Yarbanci shine babban yaren daular, amma akwai kuma yarukan da ake magana da su a ƙarƙashin daular. Ta hau kan karagar mulki ta hanyar kasuwanci da jihohin Sahel da gandun daji. Babban birninta, Ilé-Ife, ya kasance ɗaya daga cikin manyan birane a cikin ƙarni na 14 a Yammacin Afirka.

{{reflist}