Jump to content

Dorben Polytechnic

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dorben Polytechnic

Standard education at it peak
Bayanai
Iri polytechnic (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Harshen amfani Turanci
Tarihi
Ƙirƙira 1995
poly.dorben.edu.ng
kofar shiega Dorben Polytechnic
Ginin shugabanin makarantar Dorben Polytechnic

Dorben Polytechnic, Kwalejin kimiyya da Ƙere-ƙere ce mai zaman kanta wacce Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya (FME) da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE) ta amince da ita a Najeriya, Afirka ta Yamma.

Kwalejin Dorben Polytechnic wadda a da ake kiranta (Abuja School of Accountancy and Computer Studies-ASACS) tana Garam, (Garam main campus) Jihar Neja, Najeriya, da wani harabar wajen arewacin Suleja, duka a Jihar Neja. Da can ana kiranta da Dorben Polytechnic (Bwari) Abuja, tunda asalinta tana da babban harabarta/Sashenta a Bwari, Abuja (kuma anan ne aka fara aikin tantancewa). Makaranta ce mai zaman kanta, kwalejin na bayar da horon da zai kai ga ba da lambar yabo ta National Diploma (ND) da Higher Diploma Program (HND) ga ɗaliban da suke da niyyar yin aiki a matsayin akawu, fannin kwamfuta, masu gudanarwa, da manajoji.

Tarihin kafa makarantar

[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa ta a cikin shekarar 1995 kuma Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa da Ma'aikatar Ilimi ta Tarayyar Najeriya ta amince da kuma ba su izinin zama makarantar Ƙere-ƙere a shekarar 1999. Makarantar ta fara da ɗalibai 250 kawai, kamar a shekarar 2010 Dorben tana da ɗalibai sama da 3500 da membobin tsangayyu sama da 45. Kafin a ba makarantar matsayin kwalejin fasaha a shekarar 2007, sai da makarantar ta mallaki kadada (hekta) 50 na fili kuma tana da garantin banki na banki akalla naira miliyan dari da kuma samar da shirye-shiryen injiniyoyi.

A cikin watan Satumba shekarar 2008, ƙungiyar gamayyar ɗalibai ta Najeriya ta bayar da lambar girmamawa ga shugaban kwalejin, Dr A.B Ekwere.