Ekei Essien Oku
Ekei Essien Oku | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Calabar, 22 ga Janairu, 1924 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 16 Oktoba 2004 |
Karatu | |
Makaranta |
Queen's College, Lagos University of North London (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | librarian (en) , marubuci da Masanin tarihi |
Ekei Essien Oku (an haife ta ranar 1 ga watan Janairu, 1924) 'yar Nijeriya ce mai ilimin laburare, masaniyar tarihi kuma marubuciya. Ta kasance ɗaya daga cikin shugabannin sashen kula da dakunan karatu na farko a Najeriya kuma mace ta farko da ta karanci ilimin Laburare a Najeriya. Ta buga littafin ta na tarihin Nijeriya wanda ya karkata sosai bisa rayuwar turawa masu yawon bude ido da suka zo Najeriya da kuma samuwar wasu garuruwa a cikin karni na 17.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Oku ne a Calabar a cikin shekarar 1924. Ta yi karatu a Najeriya ciki har da Queen's College, Legas . Ta fara aiki ne a matsayin malama kafin ta tafi aiki a matsayin mai kula da dakin karatu sai aka tura ta London don yin karatu a kwalejin kere-kere ta Arewa maso Yamma (yanzu wani bangare ne na Jami’ar Arewacin London ). Ta dawo gida Najeriya inda ta zama mace ta farko daga Nijeriya da ta zama kwararriya a fannin ilimin laburari a shekarar 1953. Wannan ya faru ne shekara biyu kacal bayan an samu namiji na farko ɗan Najeriya mai suna Kalu Chima Okorie da ya karanci wannan fannin, a shekarar 1951. Ita ce mace ta farko da ta zama shugabar dakin karatu a Nijeriya a shekarar 1964. kuma ta rike wannan mukamin a Calabar da kuma Legas.
Rubuce-rubuce
[gyara sashe | gyara masomin]Oku ta yi bincike tare da rubuta wani littafin tarihi mai suna, "The Kings and Chiefs of Old Calabar (1785-1925)". An buga littafin a shekarar 1989. Ta yi nazarin bayanan da mishan suka ɗauka ciki har da lokacin tawayen bayi kuma ta yi imanin cewa bayin sun kasance masu mubaya'a ga iyayen gijin su.
Nasarori
[gyara sashe | gyara masomin]An kwaikwayi Oku a shirin BBC na rabin sa'a wanda yayi nazari game da rayuwarta mai suna "Ra'ayin Afirka".