Kungiyan kwallon kafa na Mayakan El-Kanemi Da turanci 'El-Kanemi Warriors FC', kungiya ce da ke zaune a garin Maiduguri, jihar Borno, kasar Najeriya. Suna buga kwallo a filin wasa na El-Kanemi . Sun kawo karshen kakar wasanninsu ta shekarar 2005 a wasan dab da kammala gasar firemiya ta Najeriya. An kuma sake su zuwa Rukunin Nijeriya 1 a shekarar ta 2007. Sun sake komawa zuwa matakin farko a shekara ta 2012. Sakamakon rikicin Boko Haram, a shekarar 2014 sun kuma yi wasannin gida a Kano. Daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2016 sun karhi bakuncin wasannin gidansu a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina kafin su koma Maiduguri da filin wasa na El-Kanemi . A ranar 17 ga watan Oktoba, shekera ta 2017, kulob din ya sanar da tsohon kocin Enugu Rangers, Imama Amapakabo a matsayin sabon kocinsu kan yarjejeniyar shekara daya.[1][2]
Tun daga 17 ga watan Afrilu shekara ta 2019
Note: Flags indicate national team as defined under FIFA eligibility rules. Players may hold more than one non-FIFA nationality.