Elelenwo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Elelenwo

Wuri
Map
 4°48′N 7°06′E / 4.8°N 7.1°E / 4.8; 7.1
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar rivers
Ƙaramar hukuma a NijeriyaPort Harcourt (karamar hukuma)
Port settlement (en) FassaraPort Harcourt
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Elelenwo gari ne, da ke a yankin babban birnin Fatakwal, Nijeriya, ƙasa a yammacin Afirka. Garin gida ne ga cibiyoyin yaɗa labarai mallakar gwamnati da dama, ciki har da Gidan Talabijin na Jihar Ribas (RSTV) da Rediyo Rivers.[1][2]

Wuri[gyara sashe | gyara masomin]

Elelenwo ya yi iyaka zuwa kudu da Eleme, bayan haka ya ta'allaka ne a tsibirin Okrika. Otigba da Woji suna kan iyakar yamma, tare da Trans Amadi a can gaba da yamma. Kasuwar Oil Mill,[3] tana kan iyakar arewa kuma Rumukurusi tana can ma arewa. Iriebe yana kan iyakar gabas kuma ƙaramar hukumar Oyigbo tana gabas da Iriebe.[4]

Dubawa[gyara sashe | gyara masomin]

Garin Elelenwo ya ƙunshi galibin gine-ginen gidaje masu haɗin gwiwa, gidajen jama'a da na masu zaman kansu, da gidajen iyali guda na salo daban-daban. Wasu gidaje a Elelenwo sun haɗa da Estate Nasara, Estate Housing Eliminigwe, Pentagon Estate, da sauransu. Ofishin ’yan sanda na Elelenwo ne kawai ofishin ‘yan sanda a garin.[5][6]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Mazauna Elelenwo suna da makarantun gwamnati da masu zaman kansu na Fatakwal, ciki akwai:

Makarantun gwamnati[gyara sashe | gyara masomin]

  • Makarantar Firamare ta Jiha[7]
  • Makarantar Sakandaren Samari ta Al'umma[8]

Makarantu masu zaman kansu[gyara sashe | gyara masomin]

Sanannun wurare[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Rivers State Television Channel 22". rstv22.tv. Archived from the original on 2014-05-19. Retrieved 2014-05-19.
  2. "Thieves Invade Elelenwo Station Of Radio Rivers …Cart Away Gen Set Parts". The Tide. 2012-01-20. Retrieved 2014-05-19.
  3. Rapheal (2019-07-02). "Many faces of oil market". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-04-26.
  4. "Elelenwo (Port Harcourt)". Wikimapia. Retrieved 2014-05-19.
  5. "Rumuibekwe/Elelenwo". The Tide. 2010-07-06. Retrieved 2014-05-19.
  6. "PH Building Collapse: NIOB Urges Prosecution Of Rogue Contractor". The Tide. 2013-08-09. Retrieved 2014-05-19.
  7. "State Primary School, Elelenwo". ministryofeducationriversstate.com.ng. Archived from the original on 2014-05-19. Retrieved 2014-05-19.
  8. "Community Boys Secondary School, Elelenwo". NigeriaGalleria. Archived from the original on 2014-05-19. Retrieved 2014-05-19.
  9. "Topline Schools Shines in 2011 WASSCE". toplineschools.com. Archived from the original on 2014-05-19. Retrieved 2014-05-19.
  10. "Moncordel International School". Nigerian Schools Directory. Archived from the original on 2014-05-20. Retrieved 2014-05-19.
  11. "Salavation Heights Secondary School - Elelenwo - Ngads: Nigeria free Classified and Business Directory". ngads.com.ng (in Turanci). Retrieved 2023-04-26.
  12. "Market Square | Online Shopping | Groceries & Household Appliances | Find More, Pay Less". Market Square (in Turanci). Retrieved 2023-05-02.