Jump to content

Emeka Ananaba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Emeka Ananaba
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Shekarun haihuwa 1945
Wurin haihuwa Obegu (en) Fassara

Cif Sir Emeka Ananaba ɗan siyasar Najeriya ne. Ananaba ya zama mataimakin gwamnan jihar Abia daga shekarar 2011 zuwa 2015 a ƙarƙashin Cif TA Orji.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ananaba a ranar 31 ga watan Maris ɗin 1945 a Obegu, a Ugwunagbo a jihar Abia a yau. Ya halarci makarantar firamare ta St. Peters Obegu daga shekarar 1951 zuwa 1959 kafin ya wuce zuwa Kings College Lagos domin yin karatunsa na sakandare daga shekarar 1959 zuwa 1963. Ya shiga aikin soja ne a cikin shekarar 1964 bayan ya kammala karatunsa na sakandare inda ya shiga makarantar horas da sojoji ta sojojin sama a Kaduna. Ya halarci Kwalejin horas da sojoji ta Najeriya Kaduna daga shekarar 1965 zuwa 1966. An ba shi muƙamin Laftanar Janar na Sojojin Sama na 189 na Combatant Regular Commission a cikin watan Yulin 1965. A lokacin yaƙin basasar Najeriya, ya yi yaƙi a ɓangaren Biafra. Ya zama kwamandan Biafra ta 8 Commando Brigade kuma ya kai matsayin Laftanar Kanar. Bayan yaƙin, Ananaba ya bar aikin soja ya karanta Pharmacy a Jami'ar Najeriya, Nsukka a cikin shekara ta 1971 kuma ya kammala da B Pharm. shekarar 1976. A cikin shekarar 1983, an naɗa shi Cif da Knight a 2001.

[1] [2]

  1. "Nigeria: Governor Orji Dumps Deputy, Picks Ananaba as Running Mate". Daily Champion. Lagos. 8 February 2011. Retrieved 8 March 2022 – via AllAfrica.
  2. Nwabughiogu, Levinus (2 May 2015). "Abia: The making of first Ngwa Governor". Vanguard. Retrieved 8 March 2022.