Eric Kelechi Igwe
Appearance
Eric Kelechi Igwe | |||
---|---|---|---|
2015 - 29 Mayu 2023 - Patricia Obila (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Najeriya, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya Harshen, Ibo | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Lauya | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Eric Kelechi Igwe lauya ne dan Najeriya kuma dan siyasa wanda ya zama mataimakin gwamnan jihar Ebonyi daga Mayu 2015 zuwa Mayu 2023. An haife shi a Ndufu Alike a Ikwo, Ebonyi. A ranar 8 ga Maris, 2022, Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori Igwe da Gwamna Dave Umahi a matsayin Gwamna da Mataimakin Gwamnan Jihar Ebonyi, bisa zarginsu da sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress yayin da suke kan karagar mulki. Kotun ta ce kuri'un da aka baiwa Umahi na jam'iyyar People's Democratic Party ne kuma ta hanyar ficewa daga jam'iyyar ofishin ya kwace nasu ne. Nan take kotun ta umarci jam’iyyar PDP da ta mika sunan dan takarar gwamnan su ga INEC ko kuma a sake gudanar da sabon zaben gwamna a jihar Ebonyi.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Appeal Court dismisses suit seeking to sack Umahi". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2022-04-02. Archived from the original on 2022-04-02. Retrieved 2022-04-02.