Eyitope Ogunbodede

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Eyitope Ogunbodede
Rayuwa
Haihuwa Owo, 23 ga Janairu, 1957 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Lagos
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da mataimakin shugaban jami'a

Eyitope Ogungbenro Ogunbodede (an haife shi a ranar 23 ga watan Janairu 1957) malami ne ɗan Najeriya kuma farfesa a fannin likitan hakora wanda ya kasance babban mataimakin shugaban jami'ar Obafemi Awolowo University, Ile-Ife, Nigeria daga shekarun 2017 zuwa 2022.[1] Shi ne kuma wanda ya kafa gidan tarihi na Dema Foundation Dental Museum, gidan kayan tarihi na hakori na farko a Afirka da aka kaddamar a shekarar 2015 wanda ke datuke da kayan tarihi na tarihin hakori na Najeriya na zamani.[2]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Ogunbodede ya halarci Makarantar Sakandare ta Owo inda ya samu takardar shedar Makarantar Yammacin Afirka a shekara ta 1976. Daga nan ya wuce Jami’ar Obafemi Awolowo inda ya sami digiri na biyu a fannin kiwon lafiya da kuma digirin digirgir (BchD) a shekarun 1981 da 1985 bi da bi. Har ila yau, yana da digiri na biyu a fannin Kiwon Lafiyar Jama'a daga Jami'ar Legas (1989) kuma ya kasance fellow na likitancin a Commonwealth a Jami'ar College London tsakanin shekarun 1991 zuwa 1993.[1]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Ogunbodede ya shiga hidimar Jami’ar Obafemi Awolowo a matsayin mai horar da likitoci a shekarar 1987 kuma ya zama farfesa a shekarar 2000. A matsayinsa na malami, ya wallafa kusan muƙaloli 100 a mujallar kimiyya da ake bita. Ya rubuta fiye da 40 Conference abstracts da littattafai 2.[1] A ranar 8 ga watan Mayu 2017, an naɗa shi Mataimakin Shugaban Jami'ar Obafemi Awolowo na 11 wanda ya ƙare a watan Mayu 2022.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 "Prof. Eyitope O.O. - Vice-Chancellor". oauife.edu.ng. Archived from the original on 2019-06-08. Retrieved 2019-06-08.
  2. "Facial marks in a dental museum". The Nation Newspaper (in Turanci). 2015-09-26. Retrieved 2019-06-08.
  3. "BREAKING: Ogunbodede named OAU's new vice chancellor". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2019-06-08.