Ezra fim ne na wasan kwaikwayo na 2007 wanda Newton I. Aduaka ya ba da umarni . An nuna shi a bikin fina-finai na Sundance na 2007 da kuma bikin fina-finai da talabijin na Panafrican na 2007 na birnin Ouagadougou inda ya lashe babbar lambar yabo.
Ezra, matashin tsohon mayaki ɗan ƙasar Saliyo, yana kokawa don gano bakin zaren da kuma komawa ga rayuwa ta yau da kullun bayan yakin basasar da ya lalata kasarsa. Rayuwarsa ta yau da kullun ta raba tsakanin cibiyar farfado da tunani da kuma kotun sulhu ta kasa da aka shirya karkashin inuwar UNO. A lokacin shari’ar gyara da Ezra ya shiga, dole ne ya fuskanci ƴar’uwarsa da take zarginsa da kashe iyayensu. Amma Ezra bai tuna kome ba. Shin Ezra zai yarda da wannan abin tsoro kuma ta haka ƴar uwarsa da al'ummar ƙauyensa za su gafarta musu?