Ezra Olubi
Ezra Olubi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ibadan, 12 Nuwamba, 1986 (37 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Babcock |
Matakin karatu | computer science (en) |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | entrepreneur (en) , Furogirama da LGBTQ rights activist (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Ezra Olubi ( an haife shi ne a ranar 12 ga watan Nuwamban, shekarar 1986) a Ibadan, Jihar Oyo. ɗan kasuwa ne ɗan kasar Najeriya, ƙwararren mai fasahar watsa labarai, injiniyan na'ura me kwakwalwa kuma mai haɓaka manahajar ɗin wayar hannu. Shine CTO kuma tare da shi aka kafa babban dandalin biyan kuɗi na yanar gizo wato Paystack.[1]
Kuruciya da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Olubi a ranar 12 ga watan Nuwamba,shekarar 1986 a Ibadan. Bayan kammala karatunsa na gaba da firamari, Olubi ya tafi Jami'ar Babcock, Illishan Remo, Jihar Ogun, kasar Najeriya, kuma ya koyi kimiyyar na'ura mai kwakwalwa tsakanin shekara ta 2002 zuwa shekarar 2006.[2]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Olubi ya fara aiki ne a matsayin Manajan IT na ma'aikatat Business Management Consultants Limited, inda ya taimaka wajen haɓaka daidaita ayyukan tallace-tallace da kuma ba da kyauta manahaja. Daga baya North Ocean Logistic and Solutions Limited ta dauke shi aiki a matsayin Mai Haɓaka manahaja na Yanar Gizo.[3]