Fatima Muhammad Lolo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fatima Muhammad Lolo
Rayuwa
Cikakken suna Fatima Muhammad Lolo
Haihuwa Patigi (en) Fassara, 1893
ƙasa Najeriya
Mutuwa 15 Mayu 1997
Karatu
Harsuna Turanci
Nupenci
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Hajiya Fatima Lolo (MON), (an haifi Fatima Muhammad Kolo a Pategi, Royal Niger Company; 19 Janairu 1891 – 15 May 1997) mawakiya ce ta Najeriya, marubuciya, kuma mai ilmin tarihi.[1]

Ƙuruciya[gyara sashe | gyara masomin]

Lolo ta yi aure sau biyu kuma ba ta iya haihuwa a cikin auren biyun da tayi ba. Ta wakilci Masarautar Nupe a yawancin bukukuwa da lokutansu. Kafin ta shahara, ta yi fice wajen yin waka ga manoma da mafarauta yayin da take rawa da faranti a hannunta. Daga baya aka kira ta da Sagi Ningbazi (Sarauniyar Mawaƙa) a yaren Nupe. Shehu Shagari ne ya karrama ta MON Member of the Order of the Niger. [2]

Lolo ta mutu tana da shekaru 106 a ranar 15 ga watan Mayu 1997, bayan gajeriyar rashin lafiya.[ana buƙatar hujja]

Waka[gyara sashe | gyara masomin]

Fatima Lolo na daga cikin fitattun mata 33 da aka buga wakokinsu a cikin littafi. [3] 

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Akande, Jadesola Olayinka Debo (1990). The Contribution of Women to National Development in Nigeria. Nigerian Association of University Women. p. 4,62, 63. ISBN 9789783065000.
  2. Book Now "World Nupe singer Hajiya Fatima Biography" [permanent dead link], Book Now Ng, 2019
  3. fetus adelayo, "Bolanle awes song women virtues" , " Punch Nigeria, 2019