Fatoumata Bâ
Fatoumata Bâ | |
---|---|
Haihuwa |
1986 Senegal |
Dan kasan | Senegalese |
Aiki | Tech, Entrepreneur |
Shahara akan | Founder of Janngo Capital |
Lamban girma |
|
Fatoumata Bâ (haifuwan 1986) ta kasance 'yar kasuwa ce ta fasaha 'yar kasar Senegal, kuma ita ce mu'assasin Janngo Capital. An jigina mata habanka Jumia, da habakar ilimi, da ci gaban SMEs ta hanyar fasaha a Afirka.[1][2][3]
Rayuwa da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Haifuwan ta a shekara ta 1986 a cikin ahalain matsakaicin matsayi a Dakar Senegal, Fatoumata ta fara son harkan fasaha tun tana 'yar shekara tara da haifuwa, lokacin da ta datse kwamfutar mahaifinta wato (hacking) a turance. Lokacin da take da shekaru 11, ta kirkiro wa kanta adireshin imel na farko, kuma a shekara 16, ta gina shafin yanar gizon ta na farko. Fatoumata tana da takadar shedar digiri ta farko daga Makarantar Kasuwanci ta Toulouse a Togo, da kuma digiri na biyu (masters) a Gudanarwa, Dabaru, Tallace-tallace, da Kudintawa daga ESC Toulouse, Faransa. Ta ci gaba da halartar Makarantar Harvard Kennedy, Amurka, don Ilimi na Zartarwa a cikin Jagorancin Duniya da Manufofin Jama'a. [4][5]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Fatoumata ta fara aikin sana'an ta a shekara ta 2007 a matsayin Manajar Asusu da Mai Habaka Kasuwanci na Index Multimedia. A shekara ta 2008, ta game da France Telecom a matsayin mai ba da shawara kan Sayarwa kuma daga baya ta ci gaba zuwa matsayin mai nazarin kasuwanci. Ta ci gaba da bunkasa aikinta a Atos Consulting, a inda ta ja ragamar Babban Mai ba da Shawara na tsawon shekaru uku (3). [6]Bayan ta dawo Afirka, Fatoumata ta kafa Jumia Côte d'Ivoire kuma ta yi aiki a matsayin CEO na shi daga shakara ta 2013 zuwa shekara ta 2015. Bayan haka, Fatoumata ta rike ragamar Shugaban Jumia Najeriya, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen fadada kamfanin da nasara a fadin nahiyar. [7][8][9][10]A halin yanzu tana aiki da Board of SouthBirdge Investment Bank kuma memba ce na Board and Investment Committee of Creadev Africa. Ta kuma shiga cikin Majalisar Mata a Afirka da Majalisar Duniya ta Duniya a kan Sabon Tsarin Tattalin Arziki.[11][12][13]
Janngo
Assasawan shekara ta 2018, Janngo Capital kamfani ne na Kasuwanci dake Ivory Coast tare da bangarori daban-daban wanda ya haɗa da kayan masarufi, kayan bukatuwa, kasuwancin gona, fasaha, sabis na kudi, da bangarorin kiwon lafiya a duk faɗin Afirka. Kamfanin ya sadaukar da kansa zuwa ga ginawa, habakawa, da sanya hannun jari a cikin zakwakuran 'yan Afirka masu "tech for good", tare da manyan ofisoshinsa a Abidjan da Paris. [14][15] Janngo Capital an san shi a matsayin mafi girman asusun fasaha wanda ya daidaita jinsi a Afirka ba tare da rinjayen wani bangare bisa wani bagare ba. Wani rukuni na masu saka hannun jari ne ke tallafawa, gami da daidaitattun cibiyoyin hada-hadar kudi na ci gaba da manyan masu saka hannun jarin kasuwanci, masu zaman kansu, kamar Bankin Zuba Jari na Turai (EIB), Bankin Raya Afirka (AfDB), da Proparco. [16][17][18]
Karramawa da sanayya
[gyara sashe | gyara masomin]- 'Matashi na Duniya' na Taron Tattalin Arziki na Duniya.
- Zaɓi Afirka 100 'Shugabannin Tattalin Arziki na Gobe'.
- Forbes Africa '30 under 30'.[19]
- Karramawar Aenne Burda don jagorancin hangen nesa, kyakkyawan fata, da ƙarfin zuciya.[20]
- Mutane 100 Masu Yawan Tasiri Mata na Afirka 2020 & 2021.[21]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Infusion, Brand (2023-05-29). "Regulatory Sandboxes in Africa". Empower Africa (in Turanci). Retrieved 2024-08-30.
- ↑ "Fatoumata Ba, Janngo: Profile and Biography". Bloomberg.com (in Turanci). Retrieved 2024-08-30.
- ↑ "Fatoumata Bâ, Founder and Executive Chair, Janngo Capital: Interview: Interview - Africa 2022 - Oxford Business Group". oxfordbusinessgroup.com. Retrieved 2024-09-03.
- ↑ "Fatoumata Ba". World Economic Forum . Retrieved August 31, 2024.
- ↑ "9 Young African Entrepreneurs to Watch". POCIT. Telling the stories and thoughts of people of color in tech. (in Turanci). 2021-06-17. Retrieved 2024-09-03.
- ↑ alm (2022-07-14). "FATOUMATA BA - Founder & Chief Executive Officer, Janngo Capital". Africa Leaders Magazine (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "Fatoumata BA". Rencontres Economiques d'Aix-en-Provence 2018 (in Faransanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ Tech pioneer in Africa: Fatoumata Bâ – DW – 10/18/2019 (in Turanci). Retrieved 2024-08-31 – via www.dw.com.
- ↑ Adegoke, Yinka (2019-11-26). "A female-led venture capital fund focused on African women founders nears its €60 million target". Quartz (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "Fatoumata Ba - Managing partner at Janngo Capital". Rest of World (in Turanci). 2022-05-11. Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "DLD Conference: Digital-Life-Design". dld-conference.com. Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "Who We Are – Janngo" (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "Fatoumata Ba". World Economic Forum. Retrieved August 31, 2024.
- ↑ Kene-Okafor, Tage (2022-09-12). "Pan-African 'gender equal investor' Janngo Capital hits first close of €60M fund". TechCrunch (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "Janngo" (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "Janngo Capital Startup Fund, Africa's largest gender equal tech VC fund reaches the first close of its €60 million new fund | Proparco - Groupe Agence Française de Développement". www.proparco.fr. Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "Private Equity International | Database". Private Equity International (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ "JANNGO CAPITAL STARTUP FUND". European Investment Bank (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ Dolan, Kerry A. "Africa's Most Promising Entrepreneurs: Forbes Africa's 30 Under 30 For 2016". Forbes (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.
- ↑ Danoglidis, Saki Athanassios (January 20, 2019). "Aenne Burda Award: Superwoman made in Africa". Hubert Burda Media. Retrieved August 31, 2024.
- ↑ "100Women | Avance Media | Fatoumata Bâ" (in Turanci). Retrieved 2024-08-31.