Jumia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Group half.svgJumia
JumiaLogo (14).png
Bayanai
Suna a hukumance
Jumia
Iri kamfani da public company (en) Fassara
Masana'anta retail (en) Fassara
Ƙasa Najeriya, Kenya, Misra, Côte d'Ivoire, Ghana, Tunisiya, Senegal, Kameru, Moroko, Uganda da Aljeriya
Aiki
Ma'aikata 4,000 (2020)
Harshen amfani Turanci
Mulki
Hedkwata Ikeja
Tsari a hukumance public company (en) Fassara
Stock exchange (en) Fassara New York Stock Exchange, Inc. (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 2012
Wanda ya samar

group.jumia.com


Facebook icon 192.pngTwitter Logo.pngYoutube-variation.pngInstagram logo 2016.svg

Jumia wata kafa ce ta yin kasuwanci na kayan wuta, kamar su wayar hannu, telebijin, computer da sauran su, da kuma kaloli daban daban na kayan sawa. Kuma ana gudanar da kasuwancinne ta hanyar yin amfani da yanar gizo-gizo. An kirkiri Jumia a shekara ta dubu biyu da sha biyu 2012 inda aka faɗaɗa ta a ƙasashe biyar waɗanda suka ƙunshi Egypt, Morocco,Ivory coast,Kenya da Kuma South Africa a shekara ta dubu biyu da sha huɗu. Kamfanin ya buɗe ofisoshi a Tanzaniya, Tunusiya, Ghana, Cameron, Aljeria da Uganda. Zuwa shekera ta dubu biyu da sha takwas kamfanin ya yaɗu a ƙasashe goma sha huɗu a yankin Africa. A shekara ta dubu biyu da sha Uku 2013 Kamfanin ya samar da Jumia travel, ɓangaren samar da hotel, da Kuma Jumia food, bangaren samar da abinci. A 2017, Jumia sun samar da Jumia one, wata manhaja da take bada damar biyan kuɗi kamar siyan kati, tura kaudi,da sauransu. Kuma sun samar da Jumia pay hanyar da za'a iya siyan kayayyakin Jumia. A yanzu haka Jumia tana ɗaya daga cikin manyan kafofin yin kasuwanci na yanar gizo-gizo musammam ma a yankin Afrika.