Jump to content

Feteer meshaltet

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Feteer meshaltet
Tarihi
Asali Misra
Feteer meshaltet
Egyptian-food-16.jpg
Feteer meshaltet in Egypt
Tarihi
Asali Misra

Feteer meshaltet (Larabcin Masar), a zahiri "pies mai taushi" ko "pies mai kamar taushi"), sau da yawa ana kiranta da meshaltet, shi kayan fulawa ne na 'yan Egypt mai laushi. Ya ƙunshi nau'o'in shinfiɗa hawa masu yawa na gurasa da man shanu ko butter da kuma abin sawa aciki in mutum na so. Abin da za'a sa zai iya zama mai zaƙi ko mai gishiri. Abubuwa masu zaƙi sun haɗa da chukwui, kwakwa, mehalabiya, malban, Nutella ko cakulat, yayin da Abubuwa masu gishiri ze iya zama komai daga naman sa zuwa sausage ko chukwui. Sau da yawa ana tsoma meshaltet wanda ba kayan haɗi a cikinsa a cikin zuma kuma ana yada shi da jam ko chukwui ko kuma ana cin sa tare da zaitun. Saboda sauƙin amfani da shi, ana kiran meshaltet sau da yawa Pizza na Masar.[1]

Feteer meshaltet ya zama muhimmiyar aba ce ta karɓar baƙi a Misira. Saboda haka, an ba wa shugaban Amurka Barack Obama lokacin da ya kai ziyara Masar a watan Yunin 2009. Iyalan Masar suna ba da shi a matsayin kyauta ga baƙi da abokai. Hakanan ana shirya shi lokacin hutu, bukukuwan aure, da sauran bukukuwan.

Mata suna gasa burodin meshaltet

Feteer meshaltet ya samo asali ne daga tsohuwar Misira, inda aka san shi da "feteer maltoot". Ana barin shi a cikin gidan bauta a matsayin hadaya ga alloli.[2]

  • Manakish
  1. Amira (November 5, 2014). "Alexandrian Feteer i.e. Pizza Feteer". Amira's Pantry. Retrieved June 26, 2018.
  2. Abu Farha, Sawsan (2015-02-03). "Feteer meshaltet "Egyptian layered pastry"". Chef in disguise. Retrieved 2018-06-26.