Fikayo Tomori
![]() | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Oluwafikayomi Oluwadamilola Tomori | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Calgary, 19 Disamba 1997 (23 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 27 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 75 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 185 cm |
Oluwafikayomi Oluwadamilola "Fikayo" Tomori (an Haife shi a 19 Disamba 1997) ya kasance kwararren ɗanwasan ƙwallon ƙafa ne, wanda ke buga wasa a ƙungiyar kulub din Chelsea. Ya wakilci ƙasar Canada da England a matakan wasan matasa.
Matakin wasa[gyara sashe | Gyara masomin]
Chelsea[gyara sashe | Gyara masomin]
2005–16: Matakin matasa[gyara sashe | Gyara masomin]
Tomori ya fara wasa a Chelsea a matakin under-8 level inda yakaiga har izuwa matakin akademy.[1] Ya kasance daga cikin matasan Chelsea waɗanda suka lashe gasar UEFA Youth League har sau biyu a jere kuma da lashe FA Youth Cup a 2015 da 2016.[1]
A 11 Mayu 2016, Tomori an sanya shi a cikin yan wasan na benci na Kulub din Chelsea tare da abokin wasansa, kamar Tammy Abraham da Kasey Palmer, a wasan da Chelsea ta buga 1–1 da Liverpool. Dukda haka, bai sami daman buga wasa ta biyu ba a Anfield.[2] A 15 Mayu 2016, A wasan Chelsea na karshen kakar 2015/16, Tomori yasamu daman buga wasa da sukayi 1–1 da Premier League champions Leicester City, inda ya canji Branislav Ivanović a minti na 60th.[3] Tomori yasamu shiga cikin waɗanda suka je ƙasar Tarayyar Amurka dan yin wasannin gabanin kaka, amma bai samu ya buga wasa ko ɗaya ba.[4] A 1 Augusta 2016, Tomori ya sanya hannu a kwantaragi na shekara huɗu a 2016–17.[5] A 12 Augusta 2016, Tomori ya sanya riga lamba 33 gabanin fara kakar shekarar wanda canji ne daga 43 da ya fara sawa da farko.[6]
Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]
- ↑ 1.0 1.1 "Fikayo Tomori". TheChels.info.
- ↑ "Liverpool 1–1 Chelsea". BBC Sport. 11 May 2016.
- ↑ "Chelsea 1–1 Leicester City". BBC Sport. 15 May 2016.
- ↑ "Summary: International Champions Cup". Retrieved 15 September 2016.
- ↑ "Tomori new deal on tour". Chelsea F.C. 1 August 2016. Retrieved 1 August 2016.
- ↑ "Squad list announced". Chelsea F.C. Retrieved 12 August 2015.