Florence Ita Giwa
Florence Ita Giwa | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 1999 - ga Yuni, 2003 - Bassey Ewa-Henshaw → District: Cross River South | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Cross River, 19 ga Faburairu, 1946 (78 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Kalabari harshe | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Dele Giwa | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Florence Ita Giwa (an haife ta a ranar 19 ga watan Fabrairu a shekara ta 1946) ’yar siyasan Najeriya ce, wacce ta kasance Sanatan gundumar sanata ta Kuros Ribas ta Kudu ta Jihar Kuros Riba.[1]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi karatu a makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kabul Polytechnic a ƙasar Birtaniya. Ta zama ma'aikaciyar jinya.
Fagen siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ita-Giwa ta shiga siyasa sannan ta zama shugabar jam'iyar NRC na jihar Delta . Bayan haka, an zabe ta a matsayin mamba a majalisar wakilai ta tarayya a shekara ta (1992 zuwa 1993), [2] kuma ta kasance mamba a kwamitin raba iko da majalisar wakilai ta shekarar (1994 zuwa 1995) Ta tsunduma cikin harkokin Bakassi, har ta sami laƙabi da "Mama Bakassi". Ita-Giwa an zabe ta a matsayin Sanatan mazabar Kuros Riba ta Kudu a watan Afrilun shekarar (1999) kuma an nada shi kwamitocin kan Dokoki da Ka’idoji, Muhalli, Harkokin Kasashen Waje, Mata, Neja Delta da Drug & Narcotics.
Bayan ficewa daga majalisar dattijai a shekarar ( 2003) ta koma jam'iyyar People's Democratic Party PDP, sannan ta zama Mashawarci na Musamman ga Shugaba Olusegun Obasanjo kan al'amuran Majalisar Kasa.
Jita-jita
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Mayun shekara ta ( 2010) akwai jita-jitar cewa kuɗade sun bace daga asusun Kwamitin Tsugunar da Bakassi, karkashin jagorancin Ita-Giwa, wanda ya nemi Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati ta binciki lamarin.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ita Giwa tayi aiki game da fataucin mutane da bautar da mata.
Lambar yabo
[gyara sashe | gyara masomin]Ta samu lambar yabo ta OON (Jami'in oda na Nijar) da lambar yabo ta The Sun Lifetime Achievement.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Florence Ita-Giwa's commitment". This Day. 8 September 2018. Retrieved 10 May 2019.
- ↑ Encomium Magazine