Folashade Adefisayo
Folashade Adefisayo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Lagos, |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da commissioner (en) |
Wurin aiki | Lagos |
Folashade Adefisayo Malama ce ƴar Najeriya ce kuma malama, kuma kwamishina a yanzu a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Legas[1][2][3][4].
Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]
Ta halarci jami’ar Ibadan inda ta samu digiri na farko a fannin ilmin dabbobi . Daga baya ta koma Jami'ar Jihar Legas inda ta sami Digiri na biyu a kan Gudanar da Harkokin Kasuwanci sannan zuwa Jami'ar Nottingham ta sake samun wani digiri na biyu a fannin Ilimi.
Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]
Folashade ta shirya wani shiri domin inganta ɗalibai a Kwalejin Kwamfuta (CBT), bayan an kullen COVID-19 a cikin jihar Legas, an shirya shirin don inganta kimanin ɗalibai miliyon 1.5 a duk faɗin jihar Legas da Nijeriya. Ta kuma ba da umarnin a daukaka darajar daliban Legas zuwa aji na gaba ta hanyar la’akari da ci gaba da tantancewar (CA Test).
Rayuwar mutum[gyara sashe | gyara masomin]
Folashade an haife ta kuma ta girma a yankin Legas da Ibadan ,su biyar ne a danginsu. Ita ce diyar fari, kuma tana son karatu da balaguro.
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "Edugist Presents a Seasoned Academic, Folasade Adefisayo, to Proffer Ways to Revive and Strengthen Public Education in Nigeria". Edugist (in Turanci). 2019-01-13. Retrieved 2020-11-11.
- ↑ "Lagos orders resumption of remaining classes in public, private schools". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-10-13. Retrieved 2020-11-11.
- ↑ "Lagos is prepared for new normal in education —Adefisayo -". Vanguard News (in Turanci). 2020-08-06. Retrieved 2020-11-11.
- ↑ "Folashade Adefisayo Archives | Premium Times Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2020-11-11.
Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]
- "Ministry of Education – Lagos State Government". education.lagosstate.gov.ng. Retrieved 2020-11-11.