Francis Otunta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Francis Otunta
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Francis
Shekarun haihuwa 29 ga Afirilu, 1958
Wurin haihuwa Afikpo
Lokacin mutuwa 30 ga Maris, 2021
Harsuna Turanci da Pidgin na Najeriya
Writing language (en) Fassara Turanci
Sana'a Malami da mataimakin shugaban jami'a
Personal pronoun (en) Fassara L485

Francis Ogbonnaya Otunta (ranar 29 ga watan Afrilun 1958 - ranar 30 ga watan Maris ɗin 2021) masanin lissafin Najeriya ne kuma mai kula da ilimi.[1] Shi ne mataimakin shugaban jami’ar aikin gona ta Michael Okpara na biyar bayan naɗin da aka yi masa a cikin watan Disamban 2015.[2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin naɗinsa a matsayin mataimakin shugaban jami'ar aikin gona ta Michael Okpara na 5, Otunta ya taɓa zama Farfesa a fannin lissafi a jami'ar Benin.[3] Ya kuma kasance tsohon Rector na Akanu Ibiam Federal Polytechnic, Unwana, muƙamin da ya rike daga 2006 –2014.[3] Prof. Francis O. Otunta ya karɓi ragamar shugabanci a matsayin mataimakin shugaban jami’ar aikin gona ta Michael Okpara, Umudike daga Farfesa. Hillary Edeoga bisa hukuma a ranar 1 ga watan Maris ɗin 2016.

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Otunta ya fito ne daga ƙauyen Amangwu Nkpoghoro da ke ƙaramar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi a Najeriya. Ya auri Bertha Otunta wanda suka haifi ƴaƴa shida tare da su.[4]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya rasu ne a wani hatsarin mota kuma an binne shi a ranar 10 ga watan Satumban 2021, a Afikpo.

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Jerin mutanen jihar Ebonyi..[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ugwu, Emmanuel (30 March 2016). "VC Decries Attempt to Drag MOUAU into Abia Politics". ThisDay Live. Umuahia. Archived from the original on 3 April 2016. Retrieved 23 May 2016.
  2. Okoro, Boniface (16 December 2015). "Prof. Otunta emerges new VC of Michael Okpara University •How he beat 31 other candidates". News Express. Umuahia. Archived from the original on 24 June 2016. Retrieved 23 May 2016.
  3. 3.0 3.1 Udeajah, Gordi (6 December 2015). "New Vice Chancellor For University Of Agriculture, Umudike". The Guardian Newspaper. Umuahia. Retrieved 23 May 2016.[permanent dead link]
  4. "From Edeoga to Otunta, MOUAU's Devt Continues". ThisDay Live. 23 March 2016. Archived from the original on 7 April 2016. Retrieved 23 May 2016.
  5. "Ex-Michael Okpara varsity VC, Francis Otunta buried, as Ikpeazu extols sterling qualities of deceased". 10 September 2021.