Jump to content

Gadar Mahaɗar Lekki da Ikoyi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gadar Mahaɗar Lekki da Ikoyi
gadar hanya da tourist attraction (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 6°27′01″N 3°27′21″E / 6.4502°N 3.4558°E / 6.4502; 3.4558
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajahar Lagos

Gadar mahaɗar Lekki-Ikoyi, gada ce mai tsawon kilomita 1.36 (0.84 mil) a jihar Legas. Gadar ta hada yankin Phase 1 na Lekki, da gundumar Ikoyi ta Legas. Gwamnan jihar Legas, Babatunde Raji Fashola ne ya kaddamar da gadar a ranar 29 ga watan Mayun 2013.

Zane da gini

[gyara sashe | gyara masomin]

Gadar dai ita ce gada ta farko da aka yi amfani da kebur wajen gina ta a Najeriya wadda kamfanin Julius Berger ta gina. Gadar tana da dakin kula mai tsawon mita 9 daga matakin ruwa domin ba da damar zirga-zirgar ababen hawa.[1]

Gadar gada ce mai dauke da titi kuma an kayyaje amfani da ita ga motocin masu zaman kansu da na yan kasuwanci wadanda ba su wuce daukan mutum 26 ba.[2] Kofar shiga ta na nan a karshen gadar Lekki. Wurin tsaron dai ya jawo cece-kuce inda wasu ‘yan Legas ke ganin cewa tun da aka gina gadar da jama’a ya kamata a rika amfani da ita ba tare da an biya ba.

A dayan bangaren kuma, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ba wai kawai ana bukatar tara kudaden ne domin kula da gadar ba, har ma da samar da kudaden gina wasu gadoji da za su hada sassan Legas. Hanyar ruwan da aka gina gadar ya kasance mallakin gwamnatin tarayyar Najeriya ne kuma ita take kula da shi.

Baya ga zirga-zirgar ababen hawa, gadar kuma tana aiki azaman wurin Nishadi. Mazaunan Lekki Phase 1 da Ikoyi masu son motsa jiki suna amfani da lungu da saqo na gadar wajen yin gudu da sassarfa, yawanci a safiya da maraice. Masu yawon bude ido da sauran masu ziyara ma suna ganin wannan gadar a matsayin daya daga cikin wuraren da ake ziyarta kuma gadar ita ce wurin da aka fi daukar hoto a Legas. Wanda ya kafa Facebook, Mark Zuckerberg ya yi dan ga jera. gudun a kan gadar Mahadar Lekki da Ikoyi a yayin ziyarar da ya kai Legas.  

  1. "Fashola commissions Lekki-Ikoyi link bridge". 29 May 2013.
  2. "Lekki-Ikoyi Bridge: A Monument for Posterity, Articles | THISDAY LIVE". Archived from the original on 2013-12-27. Retrieved 2013-11-01.