Jump to content

Julius Berger

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

[1]

Julius Berger
Bayanai
Suna a hukumance
Julius Berger
Iri kamfani
Masana'anta ginawa
Ƙasa Najeriya
Aiki
Ƙaramar kamfani na
Harshen amfani Turanci
Kayayyaki
Mulki
Administrator (en) Fassara Sumfuri
Hedkwata Abuja
Mamallaki Julius Berger
Stock exchange (en) Fassara Kasuwar Hannun Jari Ta Nigeriya
Tarihi
Ƙirƙira 1950
julius-berger.com

Kamfanin Julius Berger wani shahararren kamfanin gine-gine ne dake Najeriya wanda helkwatar ta ke a birnin Abuja da kuma wasu garuruwa kamar jihar Lagos da Uyo.[2]

Akwai ayyukan kamfanin da dama a kasar Najeriya na kere-kere da gine-gine na zamani sannan idan aka koma kudancin Najeriya akwai ayyukanta na gidajen zama da kamfanonin man-fetur da sauransu. Kamfanin sananna ce Najeriya ta ayyukanta kamar gine-gine, manyan tituna da kuma gidajen zama na ma'akatan kamfanin man fetur na Chevron dake hedikwata a Lagos.[3]

Kamfanin tana cikin jerin Nigerian Stock Exchange tun a shekarar 1991.[4] Kuma harkikin gine-gine shine ginshikin kamfanin na Julius Berger. Kuma tana da ma'aikata fiye da 18,000 a kasashe kusan 40 da abokan hulda a nan Najeriya da sauran matatun man fetur na duniya.[5][6]

Tarihin Kamfanin Berger a Najeriya ya fara ne daga shekara ta 1956 lokacin da kamdanin ta sama kwangilar gini gadar second mainland a Lagos a kan kudi naira miliyan talatin da daya da dubu dari biyu (₦31.2 million). Hakika wannan aiki ne mai muhimmanci sosai musamman saboda shine aiki na farko da aka fara da kankaren zamani. An gudanar da aikin gadan a kashi-kashi, yayinda aka kammala kashi na farkoa a 1969 sannan kuma aka gama kashi na biyu a 1974. Kamfanin tana cikin aikinta na farko ko gamawa ba ayi ba suka sama aiki na biyu na gina hanyoyi ruwa na birane a Jos wanda gwamnatin jihar Benue da ta Joss suka basa, kuma shine aikinsu na farko a yanki da ba Lagos ba. Wannan aiki ya hada da gina tafkunan na tara ruwan sama da kuma dam, wuraren tace ruwa da kuma tankunan ruwan. Aikin ginin gadan Eko na farko da sukayi ya jawo masu martaba matuka kuma yasa sun zama zabi na farko wajen gyaran gadar River Niger wacce aka lalata a lokacin yakin basasa. Wannan aiki ya sama sun zamo kullum cikin aiki a Najeriya.[7]

Lokacin da yaki ya kare, birnin Lagos ya cunkushe da yawan jama'a kuma karin sabon gadar Eko da aka gina bai wani yi tasiri ba a wajen rage cunkoso akan tituna. Domin kawo saukin cunkoso a garin, Gwamnatin Lagos ta sake ba wa Berger sabon aikin gina tituna, wannan aiki da aikin gadar Neja ya sanya kamfanin ta zamo ma'aikata na dundundun a Najeriya. Ayyukan ga kamfanin tayi a Legas sun hada da; Babban titin Badagry dake Lagos, titunan Itoikin-Ikorudu-Epe masu hannu-daya, da kuma titunan da suka kewaye garin, da babban titin Apapa zuwa Oshodi da kuma titin Agege. Kadan-kadan dai kamfanin tare da tambarinta na harafin B sukai ta kaurin suna a ayyukan gwamnati don walwalar mutane a Najeriya. Kuma wanna ya samo asali ne a dalilin gwamnatin tarayya da ta maido hankalinta wajen gyara da kuma kera sabbbin manyan tituna na kasan. Kamfanin tana daya daga cikin wadanda suka gina tituna kamar titin Legas zuwa shagamu na babban titin Legas zuwa Ibadan da kuma titin gadar Jebba.[8]

Anyi wa kamfanin Berger rijista a Najeriya dab da kammala ayyukanta na gina matatun ruwa a Jos a 1974. Kamfanin ta saida kaso 40% na hannu jarin ta ga gwamnatin Lagos da na Benue-Plateau sannan kuma bayan shekaru uku, ta sake saida kaso 20%. Bayan rikicin simintin armada da akayi a tashar jirgin ruwa na Apapa, an gayyaci kamfanin don gina sabon titi a tsibirin Tin Can (Island). A tsakanin shekarun 1970 da farkon shekarun 1980s, tana daga cikin wadanda sukayi ayyuakan manyan shagunan Aladja da kuma Ajaokuta Steel da kuma ginin sabon gwamnatin tarayya na Najeriya a Abuja.[8]

A cikin watan Augustan 1965, kamfanin wacce aka samar a Germany ta gudanar da aikinta na farko a Najeriya watau ginin gadar Eko-Bridge a Lagos, wanda Shehu Shagari ya tabbatar da aikin lokacin yana matsayin Ministan Ayyuka.[9]

A shekara ta 1991, an sanya kamfanin cikin jerin kafafen huldan Najeriya watau Nigerian Stock Exchange a matsayin "Julius Berger Nigeria Plc".

A cikin shakara ta 2001, kamfanin ta maida babban ofishinta zuwa Abuja.[10]

A cikin shekara ta 2010, Business World Magazine ta lissafo kamfanin Berger a matsayin fitacciyar kamfani na gine-gine a Najeriya.[10]

A cikin shekara ta 2012, kamfanin Watertown Energy Ltd. ta mallaki kaso 10% na kamfanin Berger wanda a da ke hannun kamfanin Bilfinger Berger GmbH, wanda ya jawo dagawar hannun jarin Berger a Najeriya zuwa kaso 60.1% A watan October, 2018 kamfanin ta sanar da sabbin tsarukanta na gudanarwa, har da canza sabon shugaban tattali.

Muhimman Ayyuka

[gyara sashe | gyara masomin]

Kamfanin ta kammala ginin Gadar Eko-Birdge a 1968, Gadar Third Mainland Bridge a 1990, da kuma fili kwallon kafa na Abuja a 2003.[11]

Tashar Jirgin-ruwa na Tsiburin Tin Can a 1977.

Titin da ya gewaye cikin garin Lagos a 1979.

Ginin Ajaokuta Steel Plant wanda aka kammala a 1990.

Titin jirgin kasa na Itakpe – Ajaokuta Ore wanda aka kammala a 1990.

Ginin dam na Challawa Gorge Dam Karaye da aka kammala a 1992.

Ginin filin jirgin saman Abuja kashi na biyu watau (Abuja International Airport phase II) wanda aka kammala a 1997.

Ginin babban ofishin Babban Bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria da aka kammmala a 2002.

Gyaran tituna da wuraren more rayuwa wanda ake kanyi har yanzu tun daga shekara ta 2008.

Pipe-jacking technology na farko a Najeriya wanda aka kammala ginata a shekara ta 2011.

Ginin National Assembly (phase III) wanda aka kammala a 2011.

Ayyuka da dama wanda suka hada da matatar Escravos GTL da aka fara gina ta a 2012.

Cigaba da ginin kamfanin Bonny Liquefied Natural Gas wanda aka fara tun 1996.

An bada contiragin gina mahadun tituna da zasu hade da gadar Niger ta biyu a Julin shekara ta 2018.

Kamfanin ke da alhakin gudanar da makarantar German School Abuja, da kuma tsohuwar makarantar German School da ke Lagos.[12]




  1. "Nnanna, Ochereome (17 October 2013). "Julius Berger: Lost the magic? - Vanguard News". Vanguard News.
  2. "Imprint." Julius Berger. Retrieved on May 6, 2017. "Julius Berger Nigeria Plc 10 Shettima A. Munguno Crescent Utako 900 108 | Abuja FCT Nigeria"
  3. "Building Bridges, Crossing Frontiers Archived2014-02-22 at the Wayback Machine
  4. "Burgis, Tom (June 8, 2010). "Nigeria cancels $420m runway contract - FT.com". Financial Times. Lagos, Nigeria. Retrieved 21 September 2012.
  5. "Top 10 Engineering and Construction Companies in Nigeria". GetInsurance. 2020-01-23. Retrieved 2020-02-06
  6. "Ngcareers. "Julius Berger Nigeria Plc Careers and Reviews". Ngcareers. Retrieved 2020-05-24.
  7. "Nnanna, Ochereome (17 October 2013). "Julius Berger: Lost the magic? - Vanguard News". Vanguard News.
  8. 8.0 8.1 "Akinsanya, Olu (January 1982). "Julius Berger and Civil Engineering Technology". The People. People's Publication: 15–17.
  9. "Ojigbo, A. Okion (1982). Shehu Shagari : the biography of Nigeria's first executive president. Lagos, Nigeria: Tokion Co. ISBN 9789783000803.
  10. 10.0 10.1 "Profile & History". Julius Berger Nigeria. Retrieved 2022-02-08
  11. "Julius Berger Fact Booklet Archived 2014-02-22 at the Wayback Machine
  12. "schulprofil_2013.pdf" (Archive). Deutsche Schule Abuja. Retrieved on 19 January 2015.