Gujarat jiha ce, da ke a Yammacin ƙasar Indiya. Tana da yawan fili kimanin kilomita
Arabba’i 196,024 da yawan jama’a 60,439,692 (in ji ƙidayar shekarar 2011). Jihar tarayyar Indiya ce daga shekara ta 1960. Babban birnin jihar Gandhinagar ne. Birnin mafi girman jihar Ahmedabad ne. Acharya Dev Vrat shi ne gwamnan jihar. Jihar Gujarat tana da iyaka da jihohin uku (Rajasthan a Arewa maso Gabas, Dadra da Nagar Haveli da Daman da Diu a Kudu, Maharashtra a Kudu maso Gabas, Madhya Pradesh a Gabas) da ƙasar ɗaya (Pakistan a Yamma).