Gundumar Sanatan Anambra ta Tsakiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Anambra Central
senatorial district of Nigeria (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaAnambra

Gundumar Sanatan Anambra ta tsakiya a jihar Anambra na ɗaya daga cikin gundumomin Sanata uku dake jihar. Tana da ƙananan hukumomi bakwai (7). Waɗanda suka haɗa da: Awka ta Arewa, Awka ta Kudu, Njikoka, Anaocha, Idemili ta Arewa, Idemili ta Kudu da Dunukofia. Tana da rumfunan zaɓe 1,556 (Pus) da wuraren rajista 109 (RAs) a lissafin shekarar 2018 Ofis ɗin hukumar INEC da ke Amawbia, ƙaramar hukumar Awka ta Kudu ita ce cibiyar tattara sakamakon zaɓe. Wannan gundumar Sanatan ta mamaye babban birnin jihar Anambra, Awka, da kewayenta. Hakanan tana da fitattun mutane waɗanda suka haɗa da ƴan kasuwa da ƴan siyasa.[1][2][3][4]

Manyan Mutane a Gundumar Anambra ta Tsakiya[gyara sashe | gyara masomin]

Uche Ekwunife, Sanata

Micheal Ajegbo, Tsohon Sanata

Peter Obi, Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, ɗan takarar shugaban ƙasa

Dora Akunyili, Tsohuwar Shugaban Hukumar NAFDAC

Tony Muonagor, Jarumi kuma mawaki

Ifeanyi Okoye, mai Juhel Kyamis Pharmaceutical

Sanannun Wurare a Gundumar Sanatan Anambra ta Tsakiya[gyara sashe | gyara masomin]

Jami'ar Nnamdi Azikiwe, Awka

Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, dake Amaku, Awka

Jami'ar Paul.

Gidan Gwamnatin Jihar, Awka

Farfesa Kenneth Dike State Central e-Library, Awka.

Jerin Sanatocin da suka wakilci Anambra ta Tsakiya[gyara sashe | gyara masomin]

Sanatoci Jam'iyya Shekarar A Majalisa Tarihin zaɓe
Mike Ajegbo Ta 4th

Ta 5th

Ta 6th
Uche Ekwunife Ta 7th

Ta 8th

Kotu ta koreta sannan aka maye gurbinta da Victor Umeh
Victor Umeh Ta 8th Shi ya kammala wa'adin Uche Ekwunife
Uche Ekwunife 2019 har yanzu Ta 9th

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "We're ready for Anambra central re-run, says INEC". TheCable (in Turanci). 2018-01-12. Archived from the original on 2020-06-07. Retrieved 2020-06-07.
  2. "Anambra Central senatorial election to proceed Saturday - INEC - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2018-01-10. Retrieved 2020-06-07.
  3. "Another Titanic Legal Battle for Anambra Central Senatorial District". THISDAYLIVE (in Turanci). 2019-03-26. Retrieved 2020-06-07.
  4. "Finally, INEC Declares Ekwunife Winner of Anambra Central Senatorial Election". THISDAYLIVE (in Turanci). 2019-02-28. Retrieved 2020-06-07.